Siyasa mugun wasa: Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi

Siyasa mugun wasa: Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi

- Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi

- Sun hade ne a garin Ibadan, jihar Oyo

- Yanzu haka dai yan siyasar fada sukeyi a tsakanin su

Rahotannin da muke samu daga kafafen sadarwar zamani suna nuni ne da cewa tawagar tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanata da ke wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta hade da ta Gwamnan jihar a yanzu Abdullahi Umar Ganduje.

Siyasa mugun wasa: Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi
Siyasa mugun wasa: Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi
Asali: UGC

KU KARANTA: Wani babban malamin addini yayi kaca-kaca da masoyan Buhari

Kamar dai yadda muka samu, tawagar fitattun 'yan siyasar dai sun hadu ne a filin jirgin jihar Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda akayi sa'a dukkan su sun je a ranar Larabar da ta gabata.

Legit.ng ta samu a wani dan binciken da ta yi na cewa Sanata Kwankwaso da tawagar ta sa sun je jihar ne a cigaba da yawon zumuncin da yakeyi da 'yan jam'iyyar sa ta PDP a kasa baki daya.

A filin jirgin dai, mun samu hotunan gwamnan yana dagawa 'yan tawagar Kwankwaso hannu inda dukan su kayi cirko-cirko.

A wani labarin kuma, Batun takarar shugabancin kasa da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ke yi da alama za ta fuskanci babbar cikas a yayin ake ta rade-raden cewa daya daga cikin kannen sa, watau Buhari Mohammed Dankwambo da aka fi sani da BHD, ya kammala shirin fita daga PDP ya koma APC.

Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Buhari Mohammed Dankwambo yace tuni ya gama yanke shawarar fita daga PDP zuwa APC din kuma yana jiran umurnin uwar jam'iyya ne kawai da zata saka ranar karbar sa da dumbin magoya bayan sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng