Da duminsa: Sabbin yan Boko Haram sama da 100 sun sake mika wuya ga gwamnatin Najeriya
- Wasu sabbin yan ta'addan Boko Haram sama da 100 sun mika wuya ga Sojoji a Borno
- Wasu kwamandoji ne suka jagoranci yan ta'addan zuwa wajen Sojoji a Gwoza
- Har yanzu gwamnatin Najeriya na nazari kan yadda zata yi da wadannan yan ta'adda masu mika wuya
Gwoza LGA, jihar Borno - Yan ta'addan Boko Haram sama da mutum 100 tare da iyalansu sun mika wuya ga hukumar Sojojin Najeriya a jihar Borno.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya auku ne a garin Gwoza, karamar hukumar Gwoza ta jihar.
An tattaro cewa wani kwamanda ne daga cikin kwamandojinsu ya jagoranci mutum 120 zuwa wajen Sojojin.
Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa wadannan yan Boko Haram sun mika wuya ne tare da iyalansu ga rundunar 26 task force brigade dake Gwoza.
An ruwaito majiyar da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina tunanin abin da muke fuskanta yanzu sakamakon mutuwar Abubakar Shekau ne; mutuwarsa ta yiwa kungiyar illa."
"Mambobin Boko Haram 120 da iyalansu sun mika wuya a garin Gwoza yau."
Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27
Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun karkashe juna yayin rikicin da ya barke tsakaninsu a Arewacin Abadam, jihar Borno lokacin da wasu ke kokarin mika wuya.
PRNigeria ta ruwaito cewa wasu yan Boko Haram da suka shirya mika wuya sun fuskanci kalubale wajen yan ta'addan ISWAP da sukayi kokarin hanasu mika wuya.
Bangarorin biyu sun yi musayar wuta ne a unguwar Gusuriya dake garin Dumbawa.
Yan Boko Haram suna kan hanyarsu ta zuwa wajen rundunar Sojin hadaka ta MNJTF ne a iyakan Nijar ranar Lahadi, 22 ga Agusta, 2021 lokacin da aka kai musu hari.
Asali: Legit.ng