Jerin Kungiyoyin kwallo 10 mafi daraja a duniya a 2021; Man City, Chelsea na kan gaba

Jerin Kungiyoyin kwallo 10 mafi daraja a duniya a 2021; Man City, Chelsea na kan gaba

  • Kungiyar kwallon Manchester City ta zama kungiya mafi daraja a duniya
  • An fahimci cewa darajar Man City ya hau ne bayan siyan sabon dan kwallon Ingila, Jack Grealish
  • Kungiyar PSG sun shiga jerin kungiyoyin bayan siyan Lionel Messi daga Barcelona

Kungiyoyin kwallon Firimiya Lig, Chelsea, Man City da Manchester United sun shiga jerin kungiyoyin kwallo mafi daraja a duniya.

Kungiyoyin Ingila biyu ke kan gaba a jerin.

A cewar Transfermarkt da ta tattara jerin, darajar jimillan yan kwallon Man City yanzu ya kai £955.6m.

SunSport ta ruwaito cewa sabon dan kwallon Ingila, Jack Grealish da Man City ta saya £100million ya bata wannan matsayi.

Chelsea ta zo na biyu sakamakon siyan dan kwallo Romelu Lukaku a farashin £97.5 million daga Inter Milan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, Messi ne na daya

Hakazalika kungiyar kwallon PSG sun hau zuwa na uku bayan sayan gwarzon dan wasa, Lionel Messi.

Manchester United ta zo na hudu bayan sanar Raphael Varane daga Real Madrid da Jadon Sancho daga Borussia Dortmund.

Jerin Kungiyoyin kwallo 10 mafi daraja a duniya a 2021; Man City, Chelsea na kan gaba
Jerin Kungiyoyin kwallo 10 mafi daraja a duniya a 2021; Man City, Chelsea na kan gaba Hoto: Chelsea FC
Asali: Getty Images

Ga jerin kungiyoyin nan:

1. Man City (Ingila) - £955.6m.

2. Chelsea (Ingila) - £898m

3. PSG (Faransa) - £894m

4. Man United (Ingila) - £835m

5. Liverpool (Ingila) - £814m

6. Bayern Munich (Jamus) - £736m

7. Real Madrid (Spain) - £700m

8. Barcelona (Spain) - £694m

9. Atletico Madrid (Spain) - £656m

10. Tottenham Hotspur (Ingila) - £633m

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng