Kotu tace ba zata hana hukuma damke Abba Kyari da mikashi ga Amurka ba

Kotu tace ba zata hana hukuma damke Abba Kyari da mikashi ga Amurka ba

  • Kotu ta yi watsi da bukatar hana hukumar yan sanda damke Abba Kyari
  • Hakazalika kotun tace ba zata hana mika DCP Kyari ga gwamnatin Amurka ta hanyar 'ex parte' ba
  • 'Ex parte' wani bukata ne da ake gabatarwa Alkali a kotu ba tare da sanin wanda aka shigar kara ba

Abuja - Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ranar Alhamis ta ki amincewa da bukatar hana hukumar yan sanda da Antoni Janar damke Abba Kyari da kuma mikashi ga Amurka.

Tuni dai an dakatar da babban mataimakin kwamishanan yan sanda, DCP Abba Kyari, kan zargin hada baki wajen damfarar wani attajirin dan kasar Qatar tare da dan damfara Hushpuppi.

Alkali Ahmed Mohammed ya yi watsi da karar da wata kungiyar Arewa, Incorporated Trustees of Northern Peace Foundation, ta shigar, rahoton Tribune.

Kungiyar ta shigar da karar ne ta hannun lauyanta, Dr Olukayode Ajulo, kuma ta bukaci kotun ta bada umurnin hana damke Abba Kyari har sai an kammala bincike da hukunci kan lamarin.

An shigar da karar ta 'ex-parte' ranar 9 ga Agusta, 2021.

A sanar da wadanda aka shigar tukun, Alkalin kotu

Bayan sauraron jawabin lauyoyi, Alkali Mohammed, ya ce ba zai bada umurnin hana damke Abba Kyari da mikashi ga Amurka ta wannan hanya ta 'ex parte' ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkali ya umurci lauyoyin su sanar da ofishin Antoni Janar da ofishin hukumar yan sanda kan wannan lamari sannan a sake zama ranar 9 ga Satumba, 2021.

Kotu tace ba zata hana hukuma damke Abba Kyari da mikashi ga Amurka ba
Kotu tace ba zata hana hukuma damke Abba Kyari da mikashi ga Amurka ba Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel