Da duminsa: An hallaka kwamandan yan sanda da wasu mutane 7 a Plateau

Da duminsa: An hallaka kwamandan yan sanda da wasu mutane 7 a Plateau

  • Har yanzu ana cigaba da kashe-kashe a jihar Flato, Arewa maso tsakiyar Najeriya
  • A ranar Litinin an sake hallaka wasu mutane 8, ciki har da kwamanda
  • Gwamnan jihar ya ziyarci Buhari don yi masa bayanin halin da jiharsa ke ciki

Jos, Plateau - Akalla mutum 8 (takwas), ciki har da babban jami'in dan sanda da dan banga aka hallaka a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau da yammacin Litinin, 23 ga Agusta, 2021.

A rahoton Punch, an bayyana sunan babban dan sandan wanda shine kwamandan rundunar leken asiri ta IRT matsyain AbdulRahman Isah.

Shi kuma dan bangan sunansa Hassan Mohammed.

An tattaro cewa an kashe wadannan mutane ne a unguwar Kwoi ta karamar hukumar Mangu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya tabbatar da wannan labari a jawabin da yayi a Jos ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Da duminsa: An hallaka kwamandan yan sanda da wasu mutane 7 a Plateau
Da duminsa: An hallaka kwamandan yan sanda da wasu mutane 7 a Plateau
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng