Kuyi hakuri da gwamnatin Buhari, Minista yayi kira matasa marasa aiki

Kuyi hakuri da gwamnatin Buhari, Minista yayi kira matasa marasa aiki

  • Bayan kunyar da Najeriya ta sha a gasar Olympics, Ministan ya baiwa yan Najeriya hakuri
  • Ya tabbatar da cewa lallai akwai matsalar rashin aikin yi a Najeriya
  • Ya nasabta hakan ga matsin tattalin arziki da rashin kudi

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya yi kira ga matasa marasa aikin yi a kasar nan suyi hakuri da gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari.

Yayinda yake jawabi kan rashin aiki dake kara yawa tsakanin matasa a shekaru shida da Buhari ya hau mulki, Sunday Dare yace rashin kudi ne ya janyo haka, saboda haka wajibi ne matasa suyi hakuri.

Ministan ya yi wannan bayani ne ranar matasan duniya yayinda yake hira a shirin 'Politic Today' a tashar ChannelsTV.

Kuyi hakuri da gwamnatin Buhari, Ministan wasani yayi kira matasa marasa aiki
Kuyi hakuri da gwamnatin Buhari, Minista yayi kira matasa marasa aiki Hoto: NTA
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Yace,

"Wannan gwamnatin tayi kokarin sauya halin da matasa ke ciki fiye da basu tallafi ko jari zuwa zuba kudi cikinsu kamar yadda akayi a fadin duniya."

A kan rashin aikin yi, Dare yace:

"Maganar gaskiya itace rashin kudi ne matsala, mun ga yadda dukiyoyin gwamnatin sun durkushe. Kuma idan kuka leka wasu kasashe inda akwai rashin aikin yi, ana hada kai ne tsakanin gwamnati, daidaikun mutane, da kungiyoyi masu zaman kansu."
"A namu bangaren, zaku ga cewa gwamnati na kokarin zuba kudi. Najeriya fa na da yawa, mutum milyan 210. Kuma matasa ne yawancin yan Najeriya. Amma muna kokarin ganin cewa mun koyawa matasa aikin hannu don su samu ayyuka masu kyau sabani dogara kan kwalin makaranta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng