Ba dan kokarin su Ahmad Joba ba, da Najeriya ta barke a 1966: Obasanjo ya yi ta'aziyya

Ba dan kokarin su Ahmad Joba ba, da Najeriya ta barke a 1966: Obasanjo ya yi ta'aziyya

  • An jinjinawa Alhaji Ahmad Joda da wasu tsaffin sakatarorin din-din-din kan hadin kan Najeriya
  • A cewar Obasanjo, sun yi wannan gwagwarmaya ne lokacin juyin mulki a 1966
  • Tsohon shugaban kasan ya siffanta Joda matsayin jajirtaccen dan Najeriya

Ota, Ogun - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda tsohon sakataren gwamnati, Alhaji ahmad Joda, da sauran manyan sakatarorin din-din-din suka kare Najeriya daga barkewa bayan juyin mulkin 1966.

Obasanjo, yayin aika sakon ta'aziyyarsa ta bakin mai magana da yawunsa, Kehimde Akinyemi, ya siffanta Joda a matsayin dan Najeriya na gaske wanda ya tabbatar da hadin kai da cigaban Najeriya.

A cewar Obasanjo,

"Na san bai cin Joda da wasu Sakatarorin din-din-din irinsa lokacin tashin tashina a 1966, da Najeriya ta yi kaca-laca. Saboda Araba ya lashi takobin raba kasar nan."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu

"Amma Ahmad Joda da sauran manyan jami'an gwamnati irinsu Philip Asiodu, Liman Ciroma, Alison Ayida ne suka tabbatar Najeriya bata balle ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba dan kokarin su Ahmad Joba ba, da Najeriya ta barke a 1966: Obasanjo ya yi ta'aziyya
Obasanjo ya yi ta'aziyya
Asali: Twitter

Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu

Kun ji cewa tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.

BBC ta ruwaito daya daga cikin 'yayan marigayin, Asma'u Joda, ta bayyana cewa mahaifinta ya rsu ne yau Juma'a a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

A cewar DT, Ahmad Joda ya rasu ne bayan jinya a asibitin FMC Yola.

Asali: Legit.ng

Online view pixel