Da duminsa: Hukumar Hisbah a jihar Kano ta samu na ta kotun mai zaman kanta
- Wata sabuwa! Hukumar Hisbah ta bude sabuwar kotu na kanta
- Hisbah ta ce tana fuskantar jinkiri da bata lokaci a sauran kotuna
- Hukumar na da hakkin dabbaka koyarwan addini da kiyaye lalacewan tarbiyya
Hukumar tabbatar da bin koyarwan addinin Musulunci ta Hisbah a jihar Kano ya samu na ta kotun mai zaman kanta.
BBC ta ruwaito Kwamandan Hisbah ta Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, da cewa wannan kotun zai saukake musu ayyukansu saboda jinkirin da suke fuskanta a kotunan jihar.
Hukumar Hizbah ta yi magana kan kayan da Zahra Bayero ta sanya
A bangare guda, Hukumar Hisbah masu tabbatar da dabbaka koyarwan addinin Musulunci a jihar Kano ta yi magana daga karshe kan hotunan da sukayi yawo na diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero.
Zahra Nasir Bayero, budurwa ce ga 'dan gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, kuma ana shirin daura musu aure.
Zahra Bayero da kawayenta sun gudanar da bikin share faggen daurin aure 'Bridal Shower' kuma hotunan shagalin sun tayar da kura.
Asali: Legit.ng