Bayan buge mota Range Rover SUV 2021, direban motar haya ya buge da haukar karya

Bayan buge mota Range Rover SUV 2021, direban motar haya ya buge da haukar karya

  • Direba ya buge mota mai matukar tsada sannan ya haukace
  • Bidiyon dake Instagram ya nuna yadda mutane suka zuba masa ido
  • Ba'a san abinda ya biyo bayan wannan diraman ba

An yi gajeruwar dirama kwanan nan a kasar Ghana yayinda wani direban motar bas ya buge mota kirar Range Rover SUV sannan ya kebe gefe guda ya fara hauka.

A bidiyon da ya bayyana a shafin Instagram, akan gan shi yana wayancewa kamar wanda ya bude da hauka.

Direban motar ya tube rigarsa sannan ya fara tsalle a gefe guda, kamar yadda bidiyon da atinkanews ta daura a Instagram.

Bayan buge mota Range Rover SUV 2021, direban motar haya ya buge da haukar karya
Bayan buge mota Range Rover SUV 2021, direban motar haya ya buge da haukar karya Hoto:@atikanews
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki

Wannan abu ya janyo hankulan mutane da dama yayinda suke kokarin ganin irin damejin da akayi.

Hadarin yayi muni da har motar Range Rover ta kife.

Ko a jikinsa, direban ya cigaba da rawarsa don kada wani yace masa ya biya kudin lalata mota mai tsada irin wannan.

Kalli bidiyon:

Mai wankin mota ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

A bangare guda, wani dan Najeriya mai wankin mota ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka kawo masa wanki zuwa wajen siyan teba da miya sannan ya yi kaca-kaca da motar.

A cikin bidiyon da @drive234 ya wallafa a TikTok, an ga mai wankin motar yana duke kan gwiwowinsa tare da rokon mai motar da ya gafarta masa.

Motar ta lalace sosai kuma saurayin ya yi nadama amma bidiyon bai nuno ko an yafe masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel