Majalisar dokokin jihar Neja ta sammaci shugabannin jami'ar Lapai kan karin kudin makaranta

Majalisar dokokin jihar Neja ta sammaci shugabannin jami'ar Lapai kan karin kudin makaranta

  • Yan majalisa sun ce kara kudin makaranta a jami'ar IBB bai dace ba
  • Kakakin majalisar ya bukaci shugabannin makarantar suyi masa bayani
  • Daliban jami'ar sun bayyana rashin amincewarsu da wannan sabon kari

Majalisar dokokin jihar Neja ta sammaci shugabannin jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida, IBBUL, Lapai, su bayyana gabanta domin bayanin dalilin kara kudin makarantar.

Wannan sakon sammaci ya biyo bayan tattaunawar da yan majalisar suka yi bayan Hanarabul Mohammed Haruna, mai wakiltar mazabar Bida II ya gabatar da lamarin a zauren majalisa.

Haruna ya ce wannan abin takaici ne musamman a lokaci irin wannan da mutane ke cikin halin yunwa, rahoton DailyNigerian.

Dan majalisan ya ce wannan abu da jami'ar tayi zai tilastawa dalibai ajiye karatu ko kuma shiga ayyukan alfasha.

Kakakin majalisar, Abdullahi Bawa, yayin jawabi a majalisa ya umurci shugabannin jami'ar gaba daya su gurfana gaban kwamitin majalisar don bayanin dalilinta.

Majalisar dokokin jihar Neja ta sammaci shugabannin jami'ar Lapai
Majalisar dokokin jihar Neja ta sammaci shugabannin jami'ar Lapai kan karin kudin makaranta Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta kara kudin jami'ar IBB daga N52,500 zuwa sama da N200,000

Hankalin dalibai ya tashi a jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai IBBUL, sakamakon karin kudin makarantar da hukumomin jami'ar suka yi.

A ranar Talata, shugabannin jami'ar sun sanar da dalibai cewa an kara kudin makarantar ga dukkan dalibai.

A cewar takardar sanarwar da Legit Hausa ta samu ranar Alhamis wacce Rijistran jami'ar, M.A Abdullahi ya rattafa hannu, dalibai zasu fara biyan kudi har N200,000.

A karin da aka yi, sabbin dalibai yan asalin jihar Neja zasu fara biyan N129,675.00 yayinda tsaffin dalibai zasu fara biyan N67,925.00.

Dalibai kuma wadanda ba yan asalin jihar ba zasu fara biyan N200,210.00 yayinda tsaffin zasu fara biyan N117,325.00.

Asali: Legit.ng

Online view pixel