Gwamnati za ta rabawa dattawa 200,000 kudi a fadin tarayya
- Gwamnati tarayya ta ce za ta rabawa dattawa 200,000 mazauna birane a Najeriya da annobar Korona ta shafa
- Shugaban shirin jin kai ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja
- Gwamnati tace za tayi amfani da rijistan talakawan dake Najeriya wajen raba kudin
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya za ta rabawa dattawa talakawa marasa aikin yi da kuma wadanda dokar kulle ta annobar Korona ta yiwa illa ga kasuwanci ko ayyukansu.
Gwamnati tace za tayi wannan rabon kudin ne ga mutane 200,000 kuma za'a fara karshen watan nan.
Shugaban shirin jin kai ta kasa, Iorwa Apera, a ranar Litinin ya bayyana hakan a taron tattaunawa da dattawa da akayi a Abuja.
Ya bayyana cewa za'a fara rabon kudin muddin mutan unguwanni suka tabbatar da sunayen wadanda aka tara.
A cewarsa, kashi 4% na talakawan Najeriya milyan 35 a rijistan talakawa na gwamnati dattawa ne, Thisday ta ruwaito.
Ministar tallafi, jinkai da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, a jawabinta ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da wannan shiri ne domin rage radadin da dattawa a Najeriya ke ciki.
Ta ce yunwa, talauci, da annobar COVID-19 ta wajabta taimakawa wadannan mutane.
Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci
Karamin Ministan Lafiya, Dr. Olorunimbe Mamora, a ranar Talata, ya yi kira ga shugabannin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD su koma teburin sulhu.
Gwamnati tace tana iyakan kokarinta wajen canza tunanin da ake mata a bangaren lafiya.
Mamora ya bayyana hakan ne a taron kungiyar likitoci NMA, shiryar birnin tarayya, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng