El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita

El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita

Shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky , da uwargidarsa, Hajiya Zeenah, na shirin fita daga Najeriya domin duba lafiyarsu.

Jaridar Punch ta ce ta samu labarin haka ne ranar Juma'a.

Majiya dake kusa da Shugaban Shi'an tace Zakzaky da matarsa na son amfani da wannan dama ne don duba lafiyarsu saboda rashin lafiyansu yayi tsanani saboda tsawon lokacin da sukayi a tsare.

Yanzu haka majiyar tace El-Zakzaky da matarsa na zaune a Abuja tun bayan sakinsu da kotu tayi.

Jita-jita sun yadu cewa Malamin ya fita kasar waje a ranar Juma'a, amma mai magana da yawunsa, Abdullahi Mohammed, ya karyata hakan.

Ya bayyanawa Punch cewa:

"Sheikh da matarsa na nan, basu yi tafiya ba. Zan sanar da ku idan akwai sabon labari."

Amma wata majiyar daban dake kusa da Sheikh Zakzaky ta bayyana cewa, "Zai yi tafiya nan ba da dadewa ba. Shi da matarsa na bukatar ganin Likitico. Akwai bukatar a dubasu."

Kara karanta wannan

Buratai fa so yayi a mika masa Igboho, amma gwamnatin kasar Benin taki: Femi Falana

El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita
El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel