Kotu ta raba Sanatan APC da kujerarsa, ta ba ‘dan takarar Jam’iyyar PDP, Jerigbe nasara
- Alkalan kotun daukaka kara sun tsige Sanata Steven Odey daga Majalisa
- Kotun ta umarci a rantsar da Jerigbe Agom Jerigbe na PDP a madadinsa
- Alkalan da suka yanke hukuncin sun umarci INEC ta ba Jerigbe satifiket
Kuros Riba – Kotun daukaka kara da ke zama garin Kalaba, Kuros Riba, ta tabbatar da Jerigbe Agom Jerigbe a matsayin zababben Sanata a Najeriya.
Alkalin kotun daukaka kara sun zartar da hukunci cewa Jerigbe Agom Jerigbe ne zababben Sanatan yankin Kuros Riba ta Arewa a majalisar dattawa.
The Nation ta samu labari cewa kotun daukaka karar ta ce ‘dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ne ya lashe zaben da aka yi a shekarar 2020.
Kotun daukaka kara ta tsige Sanata Odey
A zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar 5 ga watan Disamba, 2020, jam’iyyar APC ce ta samu nasara, ta karbe kujerar da PDP ta ke kai a wancan lokaci.
Rahoton jaridar Guardian ya bayyana cewa Alkalai uku suka saurari shari’ar zaben a karkashin jagorancin Alkali mai shari’a, Misis Chioma I. Nwosu.

Asali: UGC
Alkalan da suka zartar hukunci sun umarci hukumar INEC ta kasa da ta karbe takardar shaidar lashe zaben da ta ba Steven Odey a shekarar da ta wuce.
Chioma I. Nwosu da sauran Alkalai biyu sun yanke hukunci cewa ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Jerigbe Agom Jerigbe ne ya yi nasara a karshen shari'ar.
Jerigbe Agom Jerigbe zai canji Sanata Rose Oko
Jerigbe Jerigbe zai maye gurbin Rose Okoji Oko wanda ta rasu kwanaki. The Cable ta ce Alkalai sun ce a rantsar da Jerigbe ba tare da wani bata lokaci ba.
Sanata Rose Okoji Oko ta rasu ne bayan ta yi ta fama da cututtukan koda da hawan jini. Sanatar ta rasu ne ta na da shekara 63 a wani asisbiti a kasar Ingila.
Da wannan nasara da jam’iyyar PDP ta samu, yawan Sanatocin ta a majalisar dattawa sun kara yawa.
Asali: Legit.ng