Yanzu-yanzu: An soma caccaka tsinke a shari'ar Sheikh Abduljabbar
Wata Kotun Shari'ar Musulunci da ke birnin Kano tana can ta soma shari'ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Asali: UGC
Wakilin BBC da yanzu haka yake kotun ta Kofar Kudu a birnin Kano ya ce da alama Sheikh Abduljabbar yana cikin koshin lafiya sai dai ya dan rame.
Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin da wanda ake kara ke tsayawa.
Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.
A bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da Yahuza mohd Nura da Bashir Sabi'u, RS Abdullahi, Y I Abubakar, Zaubairu Abubakar, Ya'u Abdullahi Umar, B S Ahmad, da kuma Umar Usman.
Yadda ake zaman kotun na yau Laraba
Alkali Sarki Yola: A ranar farko da aka gabatar da kara, an karnata wa wanda ake karar laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, amma ya musanta aikata laifin, ya tambayi shaidu, lauyoyin gwamnati suka ce suna da shaidu bayan an tambaye su ko suna da shaidu.
Alkali Sarki Yola ya tambayi lauyoyin gwamnati shin sun zo da shaidun da suka ce suna da su?
Ku biyo mu don karin bayani...
Asali: Legit.ng