Da Duminsa: Gwamnatin Benin Ta Sake Maka Sunday Igboho a Kotu da Sabbin Tuhuma

Da Duminsa: Gwamnatin Benin Ta Sake Maka Sunday Igboho a Kotu da Sabbin Tuhuma

  • Gwamnatin Benin ta shigar da nata tuhumar kan ɗan awaren kafa ƙasar yarbawa, Sunday Igboho
  • Gwamnatin tana bukatar sanin ta yadda Igboho ya shigo mata ƙasa ba bisa ƙa'ida ba
  • Hakanan zata binciki dalilin shigowarsa da shirin da yayi na tada hankali a jamhuriyar Benin

Yayin da ake cigaba da shari'ar Igboho, gwamnatin jamhuriyar Benin ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume a kan ɗan awaren yarbawa, Sunday Igboho, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Punch ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin lauyoyin dake kare Igboho, Ibrahim Salami, yace tawagar su na tsammanin fara shari'ar ɗan fafutukar da gwamnatin Najeriya.

Salami ya ƙara da cewa wanda suke karewar zai cigaba da zama a Benin domin baiwa yan sandan ƙasar damar gudanar da bincike akansa.

Sunday Igboho
Da Duminsa: Gwamnatin Benin Ta Sake Maka Sunday Igboho a Kotu da Sabbin Tuhuma Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sabbin tuhumar da Benin ta shigar

Game da ƙarar da gwamnatin Benin ta shigar akan Igboho, Salami ya bayyana cewa ana zarginsa da shigowa ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, haɗa hannu da jami'an shige da fice, da kuma kokarin haddasa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya

Yace: "Da farko alkali yana son sanin yadda Igboho ya shigo jamhuriyar Benin ta hanyar da bata dace ba. Sannan kuma zasu bincike shi kan yadda ya haɗa baki da wasu ya shigo ƙasar."

"Hakanan suna son sanin tsawon lokacin da ya ɗauka a ƙasar su da kuma irin shirin da yayi wa ƙasar.

"Sannan sun shigar da tuhumar cewa ko yazo ƙasar ne ya haddasa tashin hankali da rikice-rikice."

A wani labarin kuma Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya

Sarkin Fulanin Igangan, jihar Oyo, Alhaji Salihu Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dawo da shugaban yan awaren yarbawa, Sunday Adeyemo Igboho daga jamhuriyar Benin zuwa Najeriya.

Abdulkadir, wanda ya zanta da leadership a Ilorin, jihar Kwara, ya bayyana cewa dawo da Igboho Najeriya ya zama wajibi saboda laifin da ake tuhumarsa da shi a Najeriya ya aikata su.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262