Buhari ya bada kyautar Shanu 24, kudi da buhuhunan Shinkafa ga Sojoji da Matasan NYSC
- Buhari ya godewa Sojoji da masu bautar kasa a garin Daura
- Shugaban kasa ya basu kyautan buhuhunan Shinkafa da Shanu
- Bayan kwanaki takwas, shugaban kasan ya koma bakin aiki Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa jami'an Sojoji babban kyautar Sallah lokacin bikin Eidul Adha da yayi a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, Arewa maso yammacin Najeriya.
Hakazalika shugaban kasan ya yiwa Matasa masu bautar kasa a Daura kyautar Bijimai biyu, buhuhunan shinkafa da makudan kudi yayinda suka kai masa ziyarar ban girma.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki ranar Juma'a.
Yace:
"A ranar Sallah, shugaban kasa ya hadu matasan NYSC dake bautan kasa a Daura, kuma ya basu Shanu biyu, Milyan daya da buhuhunan Shinkafa 20."
"Shugaban kasa ya bada kyautan Shanu 22 ga Sojojin dake aiki a Katsina da Daura; ya bada biyar-biyar ga barikin Sojin kasa da na Sama dake birnin jihar, sannan ya bada biyar-biyar ga Bataliyan Sojin kasa da na Sama dake Daura."
"An baiwa Sojojin dake gadin gidan shugaban kasa Shanu biyu."
Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja
Bayan mako daya a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, shugaba Muhammadu Buhari ya ya koma birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuli, 2021.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5:40 na yamma.
A jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook, Malam Garba ya zayyana irin ayyukan da Buhari yayi daga Kano zuwa Daura a wannan lokaci.
Asali: Legit.ng