Matasa sun yi fatali da buhunan shinkafa da Dan Majalisa ya ba su, sun nuna cewa aiki suke so
- A wani abin da ya zama na mamaki, gungun matasa sun ki karbar buhunan shinkafa daga wani dan majalisa
- Matasan garin Damongo a Ghana yayin da suke mayar da kayan abincin da aka ba su, sun nemi a ba su aiki wanda suke ganin ya fi muhimmanci a gare su
- Matakin da matasan suka dauka ya sanya mutane da yawa suna yaba musu a shafukan sada zumunta yayin da suke nuni da su a matsayin abin koyi ga sauran matasa
Matasan wani gari a kasar Ghana sun haifar da ce-ce-ku-ce a kan intanet kan martanin da suka yi ga wani tallafi daga wani dan majalisa ya yi musu.
A cikin bidiyon da wani mai suna @lindaikejiblog ya raba a Instagram, matasan da suka fusata a garin Damongo a ranar Litinin 19 ga watan Yuli sun dawo da buhunan shinkafa da wani dan siyasar NPP mai suna Samuel Abu Jinapors ya ba su.
Matasan sun bayyana cewa suna bukatar ayyuka maimakon abin da aka ba su. Samuel Abu Jinapors dan majalisa ne mai wakiltar mazabarsu a majalisar dokokin kasar.
Kalli bidiyon:
Kafofin sada zumunta sun nuna martani ga bidiyon
@odenigbo_ yace ce:
"Suna da hankali. Inda Matasan Najeriya ne za su dauki buhunan shinkafa suna ihu."
Wani mai amfani da @ binary_456 ya yi sharhi:
''Girmamawa !!! Idan ya kama dan majalisar ya yi duka zai shiga! "
Yayin da @geenafoodiesand ya rubuta cewa:
"Matasan Najeriya ... kuna iya gani? Yanzu da suka ki shinkafar, muna da tabbacin kuma ba za su amince da satar akwatunan jefa ƙuri'a koda bindigogi. Ku albarkace su... Afirka dole ne ta kasance mai girma."
Wani mai suna @ayam_bash ya ce:
"Matasan Najeriya za su gwammace sanya" goyon baya ga Buhari" kan kudi naira 1000 kacal maimakon tsayawa a kan azzaluman shugabanni."
@fabulosgloria ya ce:
"Shin 'yan Najeriya za su iya yin hakan? A'a ... Wadannan samari ma suna fama da yunwa amma sun mai da hankali kan ainihin bukatunsu. Ka ga abin da za su samu."
Asali: Legit.ng