Hatsarin jirgin sojin sama: Yadda kauyawa suka ceto matukin jirgin saman bayan ya duro a dajin Zamfara

Hatsarin jirgin sojin sama: Yadda kauyawa suka ceto matukin jirgin saman bayan ya duro a dajin Zamfara

  • Wadansu kauyawa a Jihar Zamfara sun yi bayanin yadda suka ceto ran matukin jirgin yakin Najeriya
  • Rahotannin sun ce jim kadan bayan kakkabo jirgin nasa, matukin ya garzaya zuwa kauyen da ke kusa don samun mafaka
  • Bayanai sun ce an ga ’yan bindigar na kai komo a kusa da inda jirgin ya fadi

Wadansu mazauna wani kauye a Jihar Zamfara (da aka sakaya sunan kauyen) a ranar Litinin sun ba da haske kan yadda suka ceto matukin jirgin saman sojin jim kadan bayan da ya yi duro sakamakon kakkabo jirgin saman yakin a ranar Lahadi.

Ba a san makomar sauran ma'aikatan cikin jirgin ba.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu cewa jirgin yakin ya fado ne kusa da wani kauye da ke kilomita 15 yamma da garin Dansadau.

Wani mazaunin kauyen ya ce:

“Matukin jirgin ya duro ne inda ya yi amfani da lemar jirgin, sannan cikin gaggawa ya nufi wani kauye da ke kusa. Bayan da mazauna kauyen suka fahimci abin da ya faru ne suka yanke shawarar boye shi domin kar ’yan bindigar su gano shi su kuma kashe shi.”

Kara karanta wannan

2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina

"An shaida ganin ’yan at’addan auke da muggan makamai suna ta zirga-zirga a kusa da inda hadarin ya faru da alama suna neman wanda ya tsira."

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dajin Kumbayana, inda jirgin ya fadi a ya kewaye jihohin Zamfara da Kebbi da Neja kuma cike yake da 'yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin Dogo Gide da wani mai suna Sani Mochoko.

Yadda kauyawa suka ceto matukin jirgin saman bayan ya duro a dajin Zamfara
Hatsarin jirgin sojin sama: Yadda kauyawa suka ceto matukin jirgin saman bayan ya duro a dajin Zamfara Hoto: NAF
Asali: Facebook

An yi amannar Dogo Gide yana da alaka da kungiyar Boko Haram.

Daily Trust ta bada rahoton cewa wadansu ‘yan bindiga sun kakkabo wani jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya mai suna Alpha Jet a ranar Lahadi amma amma hukumomi sun musanta labarin.

Sai dai, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Kakakin rundunar mayakan saman, Edward Gabkwet, ya ce an kai wa jirgin hari ne yayin da yake dawowa daga aikinsa tsakanin kan iyakar jihohin Zamfara da Kaduna.

Kara karanta wannan

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Ya ce matukin jirgin, Laftanar Abayomi Dairo, ya yi nasarar fitar daga cikin jirgin.

“Ta hanyar amfani da tunaninsa na tsira, matukin jirgin, wanda ya gamu da mummunar aman wuta daga ‘yan bindigar, ya iya kauce musu inda ya nemi mafaka a kauyukan da ke kusa inda ya jira zuwa faduwar rana,” inji shi.

Hadarin na baya-bayan nan ya kawo jimillar hadurran jirage har guda hudu a cikin shekara guda, daya daga cikinsu ya rutsa da tsohon Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng