Gwamnatin Akwa Ibom ta sanya jarabawa ranar Sallah, Musulmai sun yi ca

Gwamnatin Akwa Ibom ta sanya jarabawa ranar Sallah, Musulmai sun yi ca

  • MURIC ta yi Alla-wadai da gwamnatin jihar Akwa Ibom
  • Ma'aikatar Ilmin jihar ta ce lallai ba zata dakatar da rubuta jarabawar shiga SS3 ba

Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC, ta caccaki gwamnatin jihar Akwa Ibom kan hakikancewa kan rubuta jarabawar shiga sabon aji ranar Sallah.

Kungiyar MURIC tace gwamnatin Akwa Ibom bata shirya zama lafiya da mutanen sauran addinai a jihar ba.

Ma'aikatar Ilmin jihar Akwa Ibom ta sanar da cewa daliban dake jihar zasu cigaba da rubuta jarabawa.

Gwamnatin jihar tace jarabawar shiga SS3 a makarantun Sakandare za ta cigaba yau Sallah duk da cewa gwamnatin tarayya ta bada hutu.

MURC ta yi Alla-wadai da wannan abu da gwamnatin jihar keyi.

A jawabin da diraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya sake a shafin kungiyar, yace abinda gwamnatin tayi ya cika abin kunya.

Gwamnatin Akwa Ibom
Gwamnatin Akwa Ibom ta sanya jarabawa ranar Sallah, Musulmai sun yi ca Hoto

Yace:
"Mun girgiza kan irin nuna banbancin addinin da wasu gwamnatocin jiha ke yiwa Musulmai."

Kara karanta wannan

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

"Gwamnatin jihar Akwa Ibom na sane sarai cewa akwai Musulmai yan asalin jihar da kuma baki. Akwai yaran Musulmai a makarantun Akwa Ibom."
"Hakikancewa kan cigaba da rubuta jarabawa a ranar ya nuna cewa gwamnatin jihar bata shirya zama lafiya da sauran addinai ba.
"Hakazalika MURIC na Alla-wadai da rainin hankalin gwamnatin Akwa Ibom na watsi da umurnin gwamnatin tarayya da ta bada hutu."

MURIC ta kara da cewa shin me za'a fadi da a Arewa akayi irin haka ranar Kirismeti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel