Da yiwuwan gwamnatin Kotonou ta hana dawo da Sunday Igboho Najeriya
1 - tsawon mintuna
- Sabanin yadda aka yiwa Nnamdi Kanu, da yiwuwan Igboho ya sha
- Igboho ya arce daga Najeriya bayan harin da hukumar DSS tayi masa
- Yanzu gamayyar Yarabawa na kokarin ganin ya samu yanci
Duk da labarin cewa an damkeshi, da yiwuwan gwamnatin jamhurriyar Benin ta hana dawo da mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, Najeriya.
Mun kawo muku cewa an damke Sunday Igboho a tashar jirgin sama dake Kotonou ranar Litnin yayinda yake shirin guduwa kasar Jamus.
Amma shugaban kungiyar kare hakkin Yarabawa, Farfesa Banji Akintoye, ya bayyanawa The Nation cewa suna iyakan kokarinsu wajen ganin cewa ba'a dawo da Sunday Igboho Najeriya ba.
Ya ce hakan zai yiwu saboda kasar Benin na girmama dokokinta sabanin Najeriya.
Yace:
"Na samu labari mara dadi na cewa an damke Cif Sunday Adeyemo a tashar jirgin saman Kotonou."
"Ni da sauren masu kishin Yoruba yanzu haka na kokari bada gudunmuwanmu don tabbatar da babu wanda ya iya cutar da shi kuma muna son tabbatar da cewa an dawo da shi Najeriya."
"Abin dadin shine kasar Benin na bin doka. Mun dauki babban Lauya kuma mun yarda da shi."
"Yanzu, wajibi mu tabbatar da cewa Sunday Igboho ya samu yanci. Duk mun san babu laifin da yayi."
Asali: Legit.ng