Ba zamu daina bayar da rahoto kan matsalar rashin tsaro ba: Kungiyar gidajen jarida sun yiwa gwamnati raddi

Ba zamu daina bayar da rahoto kan matsalar rashin tsaro ba: Kungiyar gidajen jarida sun yiwa gwamnati raddi

  • Hukumar kula da kafofin yada labarai a talabijin da rediyo ta bayyana cewa gidajen talabijin sun fara kaucewa doka
  • NBC ta yi korafi kan yadda ake bayar da bayanai kan matsalar rashin tsaro
  • Mammalakan gidajen talabijin da rediyo sun mayar da nasu martanin

Mammalakn gidajen jarida na Talabijin da rediyo a Najeriya sun yi watsi da umurnin gwamnatin tarayya na cewa kafofin yada labarai su daina bayar da bayani kan hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Shugaban kungiyar Editocin Najeriya NGE, Mustapha Isah; shugaban gamayyar yan jaridan Najeriya, Chris Isiguzo; da Diraktan kungiyar dokokin kafafen yada labarai, Richard Akinnola, sun yi ittifakin cewa ba zasu bi wannan umurnin.

Sun bayyana hakan a hirar da sukayi da gidan jaridar Punch ranar Juma'a, 16 ga Yuli.

Gidajen Jarida ba zasu bi wannan umurni ba

A cewarsu, ba kafofin yada labarai ke kirkiran labarai ba, kawai suna sanar da mutane abinda ke faruwa ne.

Kara karanta wannan

Hukumar NBC ta umurci gidajen TV da Rediyo su daina bayar da bayani game da hare-haren 'yan bindiga

Sun shawarci gwamnatin Buhari ta magance matsalar tsaro maimaikon yunkurin toshewa yan jarida baki ta ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed.

Shugaban NGE, Isah, yace:

"NBC ta ce kafafen watsa labarai su daina kawata hare-hare kuma na yarda da hakan, amma ina da matsala da maganan cewa a daina bada rahotanni. Ban san abinda suke nufi da hakan ba.
"Kafafen watsa labarai ba su ke kirkiran labarai ba. Idan akwai harin yan ta'adda, zamu ruwaito. Ba zamu daina aikinmu ba duk da barazana."

Kungiyar gidajen jarida sun yiwa gwamnati raddi
Ba zamu daina bayar da rahoto kan matsalar rashin tsaro ba: Kungiyar gidajen jarida sun yiwa gwamnati raddi Hoto: Aso Villa Rock
Asali: UGC

Shima shugaban NUJ, Isiguzo, yace ba za su bari gwamnati ta toshewa kafafen yada labarai baki ba ta kowani hali.

Yace:

"Wajibi ne hukumar ta sake duba wannan umurni. NBC ta tabbatar da cewa abubuwan da take yi na muwafaqa da abubuwan dake faruwa a kasashen duniya."

Akinola kuma yace wannan umurni wani hanya ne na kokarin kwacewa yan Najeriya muryarsu.

Yace:

Kara karanta wannan

Ana so ayi amfani da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a karya tattalin Arewa – Kungiya

"Gwamnati ta gaza wajen bayar da tsaro kuma wannan hakkinmu ne mu bayyanawa duniya inda gwamnati ta gaza."

A ranar Juma'a, mun kawo muku cewa hukumar Kula da Kafofofin watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta bukaci gidajen rediyo a Najeriya da kada su bayar da cikakken bayani game da hare-haren da ‘yan bindiga da sauran masu tayar da kayar baya ke kai wa.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga watan Yuli dauke da sa hannun Francisca Aiyetan, Daraktan kula da sa ido ga gidajen rediyon a hukumar NBC ta umarci gidajen rediyon da talabijin cewa kada su “Yayata ayyukan assha na masu tayar da kayar baya, ’yan bindiga da na masu satar mutane” a cikin rahotanninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel