Daga yanzu an amince shaguna su kasance a bude a lokutan sallah a Saudiyya
- An umarci shaguna da sauran harkokin kasuwanci da su ci gaba da budewa a duk tsawon wuni har da lokacin salloli biyar a Saudiyya
- An dauki matakin hakan da nufin matakan yaki da yaduwar annobar COVID-19 a kasar
- Sannan matakin yana nufin ba a son cunkuso ko taruwar jama’a a shagunan
Shaguna da wuraren kasuwanci za su iya zama a bude a lokutan sallah a Masarautar Saudiyya, a cewar wata sanarwa da ta fito daga gamayyar ‘yan kasuwar Saudiyyar a ranar Alhamis.
Haka nan sauran harkokin kasuwanci da na tattalin arziki za su ci gaba da hada-hada a duk tsawon sa’o’i 24, gami da lokutan sallah, kamar yadda gamayyar ta fada a cikin umarnin da ta bayar, Saudi Gazette ta ruwaito.
Gamayyar ta bayyana cewa ta yanke wannan shawarar ce lura da matakan rigakafi domin dakile yaduwar kwayar cutar COVID-19, da kuma tabbatar da kare lafiyar masu shagunan da kwastomomi.
Haka nan matakin yana nufin gujewa cunkoson jama'a da taruwa a kusa da shaguna idan suka kasance a rufe a lokutan sallah.
A cikin wata sanarwa, gamayyar ta ce an dauki wannan matakin ne da nufin inganta kwarewar kasuwanci da kuma bunkasa ayyukan da ake yi tsakanin masu shagunan da kwastomominsu.
Gamayyar ta ce an yanke shawarar hakan ne bayan ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa.
"Muna fatan za ku ci gaba da bude shagunanku kuma ku ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwancin da tattalin arziki a duk lokutan aiki, kuna karbar masu sayayya da kwastomomi," in ji gamayyar a cikin umarnin da ta bayar ga shagunan da wuraren hada-hadar kasuwanci.
An umarce su da yin tsare-tsare da kuma tanadi wajen daukar matakan da suka dace na tsara aikin da samar da damar karba-karba tsakanin ma'aikata ta hanyar da ba za ta hana ma'aikata da masu sayayya da kwastomomi yin salla ba.
Asali: Legit.ng