Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace mutane da yayansu

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace mutane da yayansu

Wasu yan bindiga sun kai mumunan hari cibiyar bincike da magance cutar tarin fuka da kuturta watau National Tuberculosis and Leprosy Centre dake garin Zaria, jihar Kaduna.

A cewar rahoton Daily Trust, an yi garkuwa da ma'aikatan asibitin biyar.

Yan bindiga sun yi artabu da jami'an yan sandan dake kusa da wajen amma suka galabesu.

Wani ma'aikacin asibitin wanda aka sakaye sunansa yace sai da aka dade ana musayar wuta sosai.

Ya kara da cewa har shugaban masu gadin na cikin wadanda yan bindigan suka sace.

Yace:

"Wadanda aka sace na zama ne a gidajen dake asibitin kuma an sace su tare da 'yayansu. Saboda haka kimanin mutane goma aka sace."

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace mutane da yayansu
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace mutane da yayansu

Kakakin kungiyar ma'aikatan lafiyan cibiyar, Maryam AbdulRazaq, ta ce sun tattara sunayen mutum shida da aka sace.

Tace wannan shine karo na uku da yan bindiga zasu sace musu ma'aikata.

Tace:

Kawo yanzu inada sunayen mutum shida amma zan yi kokarin tattara sauran nan da Litinin Insha Allah. Shugaban masu gadi, Joy Yakubu da Odor da jaririyarta, Christiana, da Kasim na cikin wadanda aka sace.

Hakazalika Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, yace ana kokarin ceto wadanda aka sace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel