Biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa haramun ne, Limamin Masallacin Tarayya
Mataimakin Limamin Masallacin tarayya, Farfesa Ibrahim Maqari, ya bayyana cewa addinin Musulunci bai amince da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba.
A fatawar da yayi yayinda Tafsirin Al-Qur'ani a ranar Litinin da jaridar Dateline ta hallara, Malam Maqari ya ce biyan kudin fansa na kara karfafa makiyi.
Saboda haka, haramun ne biyan yan bindiga da masu garkuwa da mutane kudin fansa.
"Idan Allah zai hana baiwa makiya na yaki kudi don kada ka karfafesu su cigaba da yakensu, inaga mutanen da don zalunci da ta'addanci zasu kama mutum suce sai an hada musu kudi sanna zasu sakeshi, basu kudi don a saki mutum haramun ne, laifi ne, " Sheikh Maqari yace.
Farfesa Maqari ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah (SAW) inda wani mutum ya tambayesa shin ida barawo ya bukaci ya kwace kudinsa me zai yi, Manzon Allah ya fada fasa cewa kada ya bashi.
Sai mutumin ya tambaya "Shin idan ya yake ni fa", Mazon Allah yace "ka yake shi".
"Idan na kasheshi fa," mutumin ya sake tambaya, manzon Allah yace "Zai je wuta". Mutumin ya kara tambaya, "idan ya kashi ni fa" Manzon Allah yace "za ka shiga Aljannah."
A cewar malamin, wannan ya hadisi ya karfafa haramcin bada kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Asali: Legit.ng