Mai safarar kwayoyi ya hadiye nadin hodar Iblis 113 na kimanin milyan 400, an damke shi

Mai safarar kwayoyi ya hadiye nadin hodar Iblis 113 na kimanin milyan 400, an damke shi

- Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a tashar jirgin Murtala dake Legas

- Wannan karon, mutumin ya yi bahaya sau biyar inda ya kashe dukkan hodar da ya hadiya

- Masu safarar kwayoyi sun dade suna amfani da wannan hanyar wajen fita dasu daga Najeriya

Jami'an hukumar dakile muggan kwayoyi watau NDLEA sun damke wani Henry Okonkwo bayan ya yi kokarin safarar hodar Iblis daga Najeriya zuwa kasar Andalus.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

A jawabin ya bayyana cewa an damke Okonkwo ne a tashar jirgin Murtala Mohammed dake Legas ranar Lahasi bayan ya yi kashin nadin hodar Iblis 113 da ya hadiya.

Femi Babafemi ya bayyana cewa farashin hodar Iblis da Okonkwo ya hadiya zai kai N423 million.

Ya ce Okonkwo ya yi niyyar kai hodar kasar waje ta jirgi yayinda aka damkeshi.

Mai safarar kwayoyi ya hadiye nadin hodar Iblis 113 na kimanin milyan 400, an damke shi
Mai safarar kwayoyi ya hadiye nadin hodar Iblis 113 na kimanin milyan 400, an damke shi Credit: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

"Awanni 24 bayan tsareshi kuma ana sauraron yayi bahaya, mutumin wanda ya kwashe shekaru 10 a kasar Andalus ya yi kashin nadin hodar Iblis 39, sannan daga baya yayi ba hayan nadi 113," jawabin yace.

"Karin bincike ya nuna cewa ya hadiyi wannan magani ne a dakin Otal dake Igando, jihar Legas."

KU KARANTA: Suna hanamu Sallah, kullum sai sun buge mu: Cewar Daliban da suka samu kubuta a Kaduna

DUBA NAN: Sarkin Zazzau ya nada Shehu Tijjani matsayin sabon Ciroman Zazzau

A wani labarin kuwa, NDLEA, ta kama dilalin miyagun kwayoyin da ake nema ruwa a jallo a jihar Nasarawa, Sami Ashoko, kuma ta kai samame wurin ajiyar kayansa makil da miyagun kwayoyi inda aka kama buhuna 10 na da nauyinsa ya kai kilo 1.095.3 kg.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, a ranar Talata ya ce dubun wasu masu safarar miyagun kwayoyi ta cika inda aka kama su a Iyamho, karamar hukumar Etsako ta jihar Edo da haramtattun kayansu mai dauyin 1,330kg da ake niyyar kai wa jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel