Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar NURTW sun sake yin rikici a Ondo, sun lalata motocci

Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar NURTW sun sake yin rikici a Ondo, sun lalata motocci

Rikici ya barke a unguwar Oja Oba da ke Akure, babban birnin jihar Ondo a safiyar ranar Talata a tsakanin mambobin kungiyar direbobi ta Nigeria, NURTW, The Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne kimanin awanni 48 bayan yan kungiyar da ta rabu tsagi biyu sun yi rikici a Owode inda mutane da dama suka samu rauni.

A ranar Talata, an gano cewa yan kasuwa da mazauna layin Oba Adesida sun tawatse a yayin da rikicin ya barke tsakanin yan kungiyar da suka fito da makamai suna gaba-da-gaba da juna.

An kuma lalata wasu motocci sakamakon rikicin.

Ba a tabbatar da sanadin rikicin ba a lokacin hada wannan rahoton.

Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar NURTW sun sake yin rikici a Ondo, sun lalata motocci
Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar NURTW sun sake yin rikici a Ondo, sun lalata motocci
Asali: Original

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel