'Yan bindiga daɗi sun sace wani sarkin gargajiya a Rivers
-Sace-sacen mutane dai abu ne da ke cigaba da addabar ƙasar nan, musammman a Arewacin Nijeriya.
-Sai dai ba kasafai ake samun faruwar hakan ba a kudanci.
-Ko ya kai a haihu a ragaya wajen sace wannan jami'i? Ga abin da ya faru.
Ƴan bindiga sun sace sarkin gargajiyar ne a garin Ikuru da ke ƙaramar hukumar Adoni a jihar Rivers.
Jaridar Daily ta dai rawaito cewa an sace wannan sarki ne a gidansa da ke Ikuru cikin ranakun ƙarshen sati.
Wata majiya daga fadar sarki ta tabbatar da wannan al'amari ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a ranar Lahadi.
Majiyar ta ƙara da cewa an sace sarkin kuma har izuwa yanzu ba a san inda yake ba.
majiyar ta tabbatar da cewa har wannan lokaci, waɗannan ƴan bindiga ba su kira iyalansa ba, don haka suke kira ga jam'ian tsaro da su kai masa ɗauki gudun ka da wani abu ya same shi.
Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar, SP Nnamdi Omoni, ya bayyana cewa rundunar na kan ƙoƙarinta na wajen ganin sun ceto shi, inda ya ce, "Ina mai tabbatar muku cewa kowanne jami'i na kan yin ƙoƙarinsa wajen ganin an saƙo shi."
KU KARANTA: Cbn za su habaka tsarin gudanar da kasuwar bit-coin
Haka kuma, ƴan bindiga sun sace wani malamin jami'a, Dr. Jones Ayauwo, daga sahen Nazarin Harsuna da Labarai Linguistics and Communications Departmentna Jami'ar Fatakwal (University of Port Harcourt).
Har'ila yau, ana zargin wasu ƴan bindiga daɗi da kai wa wasu ƴan jaridu uku hari a jihar ta Rivers da ke aiki da gidan talabijin ɗin jihar (Rivers State Television Authority) tare da ƙwace musu wayoyin hannu. Wannan abu ya faru ne a ranar Lahadi a kusa da Bori a ƙaramar hukumar Khana.
Daily Sun ta rawaito cewa suna kan hanyarsu ta dawowa ne daga Fatakwal a ƙaramar hukumar Andoni a lokacin da suka far musu.
Wata majiya ta ba da sunayen waɗannan ma'aikata kamar haka: Cletus Enerujama , a mafassari, da Godspwer Anele, ma rahoto, sai kuma Thursday Dick, mai ɗaukar hoto.
KU KARANTA: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC
Majiyar ta ƙara da cewa, "ma'aikatan sun yi kwance ne a gaban ƴan bindigar su huɗu a garin na Adoni tare da rasa wayoyi da kyamara da wasu muhimman abubuwa nasu da aka sace."
"Shi ma wancan shugaban sashen na Nazarin Harsuna na UNIPORT, Dr. Jones, ba a san a ina yake ba tun bayan sace shi da aka yi."
Majiyar ta tabbatar da cewa su kuma ma'aikatan RSTV sun je ofishin ƴan sanda ne daga baya domin sanar da abin da ya faru.
Kakakin Rundunar ƴan sandan, SP Nnamdi Omoni, yana tsimayin muhimman bayanai a kai waɗanda za su taimaka masa.
A bangare guda, karamar Ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Tijjani Aliyu, ta dakatar da Sarkin kasar Anagada da ke karamar hukumar Gwagwalada.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin Mai martaba Alhaji Alhassan Musa ne da taimaka wa masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayya.
Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta bayyana haka a wajen taron tsaro na gaggawa da aka shirya da masu sarautar gargajiya da sarakunan da ke Abuja a jiya.
Asali: Legit.ng