Matashi zai shafe wata 6 a gidan yari saboda bude shafin Facbook da sunan Buratai

Matashi zai shafe wata 6 a gidan yari saboda bude shafin Facbook da sunan Buratai

- Wani matashi ya debo ruwan dafan kansa bayan an same shi da laifin bude shafin Facebook da sunan Buratai

- Matashin, mai sana'ar saka faifan garmaho a gidan rawa, yana sojan gona da sunan Buratai domin damfarar mutane

- Kazalika, an gano cewa matashin ya mallaki wani shafin na Facebook da sunan diyar Dangote, Mariya Dangote

Wani Matashi mai saka faifan garmaho a gidan rawa (wato DJ) zai shafe wata shida a gidan yari bisa samunsa da laifin bude shafin Facebook da sunan tsohon hafsan rundunar soji, Laftanal Janar Tukur Buratai.

Kazalika, an samu matashin da laifin sake bude wani shafin na Facebook da sunan Mariya Dangote, diyar hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da matashin a gaban kotu bisa zarginsa da zambatar jama'a ta hanyar nuna cewa shine Buratai ko Mariya Dangote.

An gurfanar da shi a gaba kotun Jastis Mohammed Tukur da ke jihar Kaduna bisa tuhuma guda daya mai nasaba da zamba ta hanyar sojan gona.

EFCC ta ce jama'a ne suka ankarar da hukumar har ta kai ga reshen ofishinsu da ke Kaduna ya samu nasarar kama matashin.

Matashi zai shafe wata 6 a gidan yari saboda bude shafin Facbook da sunan Buratai
Matashi zai shafe wata 6 a gidan yari saboda bude shafin Facbook da sunan Buratai
Asali: Twitter

Matashin mai suna Blessed Michael, dan asalin jihar Edo da ke zaune a Kaduna, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa bayan an karanta masa a gaban kotu.

"Saboda yin basaja tare da yin sojan gona da sunan Tukur Yusuf Buratai (tsohon hafsan rundunar sojoji) da Mariya Dangote (diyar Aliko tare da zambatar jama'a ta hanyar yin hakan, ka aikata laifin da ya ci karo da sashe na 308 na kundin laifukan yanar gizo a Kaduna.

Daga bisani kotun ta yanke masa hukucin daurin wata shida a gidan yari bayan ya amsa laifinsa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Babbar kungiyar Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta ce ta gaji da cin kashi da barazanar da ake yi wa mambobinta kuma a halin yanzu tura ta kai bango.

Rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake kara samun yawaitar kai hare-hare akan makiyaya da ke zaune ko xiyartar kudancin Nigeria.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Saleh Alhassan, ya ce makiyayan da ake kashewa daban da wadanda suke tafka barna a sassan Nigeria.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel