Bidiyo: Jama'a sun yi wasoso yayin da Yahoo Boys suka yi watsin kudi a Benin
- Jama'a sun yi tururuwar wasoson kudi yayin da 'yan damfarar yanar gizo (Yahoo Boys) suka yi ruwan kudi
- A karshen makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta haramta duk wata hulda da sulallan yanar gizo
- Babban bankin kasa (CBN) ya ce ya haramta amfani da sulallan ne saboda gano yadda 'yan damfara ke amfani da su ta haramtattun hanya
Jama'ar gari maza da mata sun yi wasoson kwasar kudaden da wasu 'yan damfara ta yanar gizo da aka fi sani da 'Yahoo Boys' suka dinga watsawa a kan titi a Benin, babban birnin Jihar Edo.
Matasan sun rufe kan hanya da motocinsu tare da yin ruwan kudi, lamarin da ya haddasa cunkuso da rufe hanyar ababen hawa.
Idan ba'a manta ba, babban banki kasa (CBN) ya fitar da sanarwar hakan a makon da ya gabata inda ya umarci dukkan bankunan da ke fadin kasar nan da su rufe wani asusu da ake amfani da shi wajen harka da ''Crypto''.
Wani rahoto da jaridar Thisday ta wallafa ya bayyana cewa hukumar tsaron kasar Amurka (FBI) ce ta yi wa gwamnatin tarayya korafi akan yadda 'yan Nigeria ke damfarar kasashen turai makudan miliyoyi.
FBI ta sanar da gwamnatin tarayya cewa miliyoyin daloli daga kasashen nahiyar turai na shigowa Nigeria ta barauniya kuma haramtacciyar hanya, wanda hakan kan iya haifar da babbar matsala ga tattalin arfzikin kasa.
KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: El-Rufai ya maida wa Sheikh Gumi martani
Rahoton ya kara bayyana cewa FBI ta nuna cewa 'yan damfara da ake kira ''Yahoo Boys" sun damfari dumbin mazauna kasashen turawan yamma.
A cewar FBI, Yahoo Boys sun yi amfani da salo da dabarun damfara wajen tattare miliyoyin daloli da aka rabawa jama'a a matsayin tallafin annobar korona a kasashen turai tare da shigo da su Nigeria.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, "masu damfarar turawan yamma suna shigo da kudin da yawansu ya kai tsakanin dala miliyan $200 da dala miliyan $300 a kowanne sati, ta hanyar amfani da crypto currency".
KARANTA: Kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu
"An ankarar da gwamnatin tarayya da CBN akan abubuwan da ke faruwa wanda hakan shine yasa aka dauki matakin gaggawa domin ganin tattalin arzikin kasa bai samu wani lahani ba," kamar yadda Arise News ta rawaito.
Wata babbar matsala ta Crypto, a cewar gwamnatin tarayya, shine yadda yanzu masu garkuwa da mutane suka fara amfani da shi wajen karbar kudin fansa.
Jami'an tsaro suna matukar wahala kafin su iya gano mutumin da ya ajiye kudi ko kuma aka biya shi kudi ta hanyar amfani da Crypto saboda tsananin sirri da boye hanyoyin sauya sulallan zuwa takardu na zahiri bayan sun shiga bankuna.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.
Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.
Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng