Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 18 a garin Kuyello da ke daura da Katsina

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 18 a garin Kuyello da ke daura da Katsina

- Akalla mutane 18 ne suka rasa ransu a wani kazamin hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Kuyello da ke karamar hukumar Birnin Gwari

- Daily Trust ta rawaito cewa 'yan bindigar sun shafe kusan awanni uku suna tafka barna a kauyen

- Ya zuwa yanzu rundunar 'yan sanda da gwamnatin jihar Kaduna basu fitar da sanarwa dangane da kai harin ba

Wasu 'yan bindiga sun kashe mutane 18 a kauyen Kutemeshi da ke masarautar Kuyello a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa maharan sun shafe awanni uku suna cin karensu babu babbaka, ba tare da jami'an tsaro sun kawo agaji ba.

Abdulrahman Yusuf, kansilan da ke wakiltar mazabar Kuyello, ya tabbatar wa da Daily Trust kai harin tare da bayyana cewa an raunata mutane 15 yayin harin.

"An kashe mutane 18 yayin da wasu mutane 15 suka samu raunuka. Wadanda suka samu raunuka za'a mayar da su asibitin Kaduna domin a duba lafiyarsu. Yanzu haka shiri muke yi na binne gawarwakin mutanen da muka rasa," a cewarsa.

A cewarsa, akwai nisan kilomita hudu a tsakanin kauyen Kutemeshi da garin Sabuwa da ke jihar Katsina.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 18 a garin Kuyello da ke daura da Katsina
Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 18 a garin Kuyello da ke daura da Katsina
Source: Twitter

Ya kara da cewa 'yan kungiyar agaji ta bijilanti ne kadai suka kawowa mutanen kauyen agaji yayin da 'yan bindigar suka kawo harin.

Abdulrahman ya ce mutanen garin suna ciki mawuyacin hali saboda basu san me zai faru ba nan gaba.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran wayar Daily Trust ba.

Kazalika, kwamishinan harkokin da suka shafi tsaro a jihar Kaduna, Samuel Aruwan, bai bayar da amsa ga sakon da Daily Truust ta aika ta layinsa na wayar hannu ba.

Karamar hukumar Birnin Gwari da wasu sassan Jihar kaduna sun yi kaurin suna wajen yawaitar samun rahoton cewa 'yan bindiga sun kai hari.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa masu garkuwa da mutane cikin kakin soji sun ci karensu babu babbaka a garin Tungan Maje da ke Gwagwalada a Abuja inda suka shafe awanni suna yin yadda suke so.

Wani Shaidar gani da ido ya bayyana cewa 'yan bindigar sun shafe akalla awanni uku suna cin karensu babbaka a garin.

Daga cikin mutane hudu da 'yan bindigar suka yi awon gaba da sub akwai tsohon mataimakin shugaban hukumar NIS, Ibrahi Idris, da mutane biyu daga cikin iyalansa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel