Shin menene hukuncin Adashi a Musulunci? Daga Sheikh Bello Mai Iyali

Shin menene hukuncin Adashi a Musulunci? Daga Sheikh Bello Mai Iyali

TAMBAYA: Menene hukuncin yin Adashi a Musulunci? Wato mutane su taru suna hada kudi duk wata domin ba daya daga cikinsu har tsawon yawan su? Sannan mene ne hukuncin irin wanda ake tarawa amma mai tarawar zai karbi na wasu ranaku cikin abin da ka tara a wata daya.

Daga Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW. Babban Malami Al-Sheikh Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar lemo, Kano, ya bada fatawa akan wani bangare na wannan tambaya kamar haka, don haka zamu dibo daga cikin kalamansa don amsar tambayoyinmu.

Zan fara da jinjina ga bawan Allahn da ya rubuto mana wannan tambaya, domin kuwa, da dama daga cikin mutane suna zaton cewa irin wadannan mas’aloli babu abin cewa a kansu a addinin musulunci, wasu mu’amaloli ne da zamani ne kadai ya zo da su, babu su a musulunci, don haka ma mutane ba su cika tambaya akan hukuncinsu ba.

To amma duk wanda yake karatu kuma yake bibiyar malamai yasan cewa babu wani abu ko wata mu’amala ta zamani, face akwai hukuncinta a musulunci, ko dai tun da can malamai sun yi bayaninta, ko kuma a yanzu malamai sun tattaunata sun yi bayanin hukuncinta a musulunci, daga cikin irin wannan mas’aloli akwai adashi.

An fara yin adashi tun a karni na tara bayan hijira, ana kiransa da suna a wancan lokacin a larabce da (Al-juma’a) saboda akan yi dauka ne duk ranar Juma’a, kuma mata ne a wancan lokacin suke yi, inda duk ranar Juma’a zasu hadawa dayansu kudin da suka yi yarjejjeniya zasu ba junansu, wata Juma’ar kuma a ba wata, har a zagayo (Duba Hashiyatul Kalyubi 2/ 258).

A yau kuma ana kiran Adashi a larabce da sunan (Jam’iyyatul Muwazzafin) wato jam’iyyar ma’aikata, saboda galibin masu yin sa ma’aikata ne, kuma su ne ma suka farfado da shi, saboda su ne suke da albashin dindindin a kowane karshen wata, don haka wadanda suke aiki a wuri daya sukan yi yarjejjeniya akan duk wata zasu hada kaza daga cikin albashinsu, su ba dayansu, wani watan kuma za a ba wani, da haka har a kewayo, da sharadin ba wanda zai fita har sai an gama.

Adashi ya kasu gida biyu : Kaso na farko, shi ne wanda bayaninsa ya gabata, wato wasu mutane su hadu akan kowanne zai rika bada wani kaso na kudi da suka ayyana, a karshen kowane sati ko wata ko kullun, a ba daya daga cikinsu, haka wani watan ma za a hada a ba wani, har dai a zagayo, kuma wanda bai dauka ba yanada damar ya janye, wanda kuwa ya dauka to bai da damar ya janye har sai an gama.

Kala na biyu: kamar dai na farko, sai dai da sharadin ba wanda zai fita sai an gama, kuma an maimata sau biyu ko sau uku, ko sau kaza, kuma za a juya ne wajan karbar, na farko zai koma na karshe, na biyu na biye masa haka dai.

Malamai sun yi sabani akan kaso na farko. Mafi yawancin malamai sun halatta shi, daga cikinsu, akwai babban malamin nan Abu Zur’a Al-iraki, da Sheikh bin Baz, da Sheikh Usaimin (Allah ya jikansu da rahamarsa gaba dayansu) da mafi yawancin manya – manyan malaman.

Shin menene hukuncin Adashi a Musulunci? Daga Sheikh Bello Mai Iyali
Shin menene hukuncin Adashi a Musulunci? Daga Sheikh Bello Mai Iyali
Source: UGC

Dalilansu kuwa su ne:

1. Saboda mu’amala ce da take akwai taimakon juna da tausayawa a cikinta. Allah Madaukakin sarki kuwa tuni ya yi umarni da taimakon juna akan aikin alheri, inda yake cewa “Ku taimaki juna akan aikin alheri da tsoron Allah” (Alma’ida : 2)

2. Dalili na biyu, shi ne Asalin abubuwan da suke ba ibada ba ne halal ne yin su a musulunci, sai in Nassi ya haramtasu, to Adashi yana kan wannan asali, saboda babu wani nassi na shari’a da ya sabawa.

3. Dalili na uku, a cikin yin dashi akwai kare mutane daga afkawa cikin riba da sauran cinikayya na haramun.

Wadannan sune dalilan wadanda suka halatta wannan nau’i na adashi. Wasu kuwa daga cikin malamai sun haramta wannan nau’i, sun kafa hujja da cewa bashi ne da ya jawo amfani, don haka ya zama haramun. Kuma ciniki biyu ne cikin kama daya, kuma yana tattare da garari. Duba da dalilan da suka gabata zamu iya fahimtar cewa babu haramci akan wannan nau’i na dashi, wato halal ne. Sannan manyan malamai sunce dalilan haramta Adashi dalilai ne marasa karfi.

Idan muka koma kan kalar adashi na biyu kuwa, wanda ake shardanta cewa ba wanda zai fita har sai an gama an maimaita sau daya ko sau biyu ko sau kaza, gwargwadon dai yadda suka yi yarjejjeniya. Anan malamai sun kasa wannan nau’in gida biyu. Na farko a sanya sharadin ba wanda zai fita har sai an gama, to wannan babu laifi akan haka. Amma sanya sharadin cewa ba wanda zai fita har sai an maimaita sau kaza, to wannan haramun ne, saboda kamar ka bawa mutum bashi ne ya mayar maka, sannan ka tilasta shi cewa sai ya kara baka wani sau kaza, wannan haramun ne.

A takaice dai adashi a musulunci ya halatta, kuma babu laifi a yi sharadin ba wanda zai fita har sai an gama.

Sannan mene ne hukuncin irin wanda ake tarawa amma mai tarawar zai karbi na wasu ranaku cikin abin da ka tara a wata daya.

Lallai ne idan akaba mutum aiki, to abiyashi ladan aikinsa kamar yadda akiyi yarjejeniya. Idan masu adashi suka wakilta wani akan Tarawa da ajiya ko karbowa da hadawa kuma sukayi yarjejeniyan abinda za’a biyasa, suka yarda shima yayarda, to wannan halal ne.

Hakanan kuma idan me Adashin Gata ne, wato wanda mutum zai yi tari a wajen mai adashin ana rigista akati, shima yarjejeniya ne tsakaninsu akan abinda za’a biya mai Adashin Gatan. Yin haka kuma ba laifiba ne, halal ne.

A karshe yana da kyau mai shiga adashi ya kiyaye da abubuwan da zasu zo:

1. Ya zama an gina shi akan taimakawa juna, kada a gina shi don a cutar da wani ko wasu.

2. kada a nemi wani ya yi kari akan abin da aka bashi, saboda zai fara dauka, ko kuma zai yi jinkiri, idan ko aka ce za a baka dubu daya akan kai kuma zaka biya dubu daya da dari daya, to wannan ya zama riba, ba ya halatta.

3. Kada mutum ya shiga adashi da niyyar in ya karba ya gudu, ko ya daina zubi, saboda Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Duk wanda ya karbi dukiyar mutane da niyyar ya biya, to Allah zai biya masa (wato zai horre masa ya biya. Idan kuwa ya mutu Allah zai kawo wanda zai biya masa, ko kuma Allah ya biya masa a ranar kiyama) wanda kuwa ya karba da niyyar ya batar da shi, ya ki biya, to wannan Allah zai lalata shi” (Bukhari 2387).

Allah ya taimaka mana. Amen.

Source: Legit.ng

Online view pixel