Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan

Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan

Watan Ramadana ya kasance wata na musamman ga dukkanin Musulmi a fadin duniya. Musulmai kan jajirce wajen neman kusanci ga Allah.

Wasu kuma kan tafi kasa mai tsarki domin yin Umarah da yin dawafi ga Allah a gaban Ka’aba.

Don raya wannan wata mai albarka ta Ramadan, wasu manyan fuskoki a masana'antar kannywood suka garzaya zuwa kasar Saudiyya.

Wasu daga cikin manyan jaruman fina-finan hausa da suka halarci kasa mai tsarki sun hada da Hadiza Gabon, Hafsat Idris, Baballe Hayatu, Mc Ibrahim sharukhan, Maryam Yahaya da Ado Gwanja.

KU KARANTA KUMA: Kalli wata yar Kirista dake bayar da kyautar abinci ga musulmai a yayin bude bakin azumin Ramadan a jihar Lagas

Ga hotunansu a kasa:

Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan
Baballe Hayatu yayin da yake bude baki a kasar Saudiya

Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan
Ado Gwanja

Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan
Mc Ibrahim Sharukhan

Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan
Hafsat Idris da Hadiza Aliyu Gabon

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata yar Najeriya ta dauyin taimakawa Musulmai a wannan lokaci na Ramadana.

Matar mai suna Olashile Aboyemi na rarraba kayayyakin abinci ga Musulmai a yayin bude baki. An tattaro cewa wannan matashiya na aikata wannan aiki na alkhairi duk da cewar ita Kirista ce da addininta ya sha bambam da na Musulman.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng