Kotu ta bawa gidan yarin Kaduna umarnin gaggauta sakin matar Sheikh Zazaky
- Babbar kotun Kaduna ta umarci mahukuntan gidan yarin Kaduna su saki Zeenat, matar Sheikh El-Zakzaky domin a duba lafiyarta
- A makon jiya ne Mohammed, dan Sheikh Zakzaky, ya sanar da cewa mahaifiyarsa, Zeenat, ta kamu da cutar korona amma an hana fita da ita zuwa cibiyar killacewa
- Lauyan Sheikh El-Zakzaky, Femi Falana, ya gabatar da sakamakon gwaji da takardun asibiti da suka nuna Zeenat na bukatar kulawa saboda yanayin lafiyarta
Wata babbar kotu da ke Kaduna ta umarci hukumar gidan yarin Jihar ta gaggauta sakin Zeenat, matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban darikar 'yan uwa Musulmai na Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da ''Shi'a''.
Kotun ta bayar da umarnin ne domin a mayar da Zeenat zuwa cibiyar killace masu cutar korona bayan tabbatar da cewa ta kamu da kwayar cutar.
A hukuncin da ta yanke ranar Litinin, kotun ta bayar da umarnin a gaggauta mayar da Zeenat zuwa cibiyar killacewa mallakar gwamnati domin ta fara karbar maganin cutar korona.
KARANTA: Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin gwamnatin Buhari tun bayan hawa mulki a 2015
A makon jiya ne dan Sheikh Zakzaky, Mohammed, ya sanar da cewa mahaifiyarsa, Zeenat, ta kamu da kwayar cutar korona a gidan yarin Kaduna amma mahukuntan gidan sun ki sakinta domin a duba lafiyarta.
Tun shekarar 2015 gwamnati ta tsare El-Zakzaky tare da matarsa biyo bayan wata arangama a tsakanin magoya bayan IMN da dakarun rundunar soji a garin Zaria, Jihar Kaduna.
Femi Falana, lauyan El-Zakzaky, ya gabatar da takaradun sakamakon gwajin Zeenat da sauran takardun asibiti da suka tabbatar da cewa tana bukatar kulawa ta musamman saboda yanayin lafiyarta.
Babban lauyan, mai lambar 'SAN', ya roki kotun ta yi la'akari da shaidun da ya gabatar wajen bayar da umarnin sakin Zeenat domin ta samu kulawa a cibiyar killacewa kamar yadda hukumar NCDC mai yaki da cututtuka ta tsara tun bayan barkewar annobar korona.
A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa wani mayakin kungiyar Boko Haram da aka kama ya bayyana cewa Shekau ya samu nakasa a kafafunsa, a saboda haka ba ya iya tafiya daidai.
Matashin mayakin mai suna Mohammed Adam, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng