Kwamishinan 'yan sandan Ebonyi ya kama hadiman gwamnan jihar biyu da shugaban karamar hukuma

Kwamishinan 'yan sandan Ebonyi ya kama hadiman gwamnan jihar biyu da shugaban karamar hukuma

- Rundunar 'yan sanda ta kama wasu hadiman gwamnati da zababbun 'yan siyasa na karamar hukumar Ohaukwu

- Kwamishina 'yan sandan jihar Ebonyi ne ya shiga har wurin taron masu ruwa da tsaki ya fito da mutanen tare da tafiya da su

- Mataimakin gwamnan jihar Ebonyi ne ya kira taron sulhu tare da gayyatar masu ruwa daga yankin

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba, ya kama shugaban karamar hukumar Ohaukwu, Clement Odah, da mamba mai wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jihar, Chinedu Awo, bisa zarginsu da hannu a kisa da barnar dukiya da aka yi a yankin.

Kazalika, rundunar 'yan sanda ta kama wasu sauran hadiman gwamnati da masu ruwa da tsaki a yankin har su 30, wadanda suka hada da shugaban kungiyar cigaban Effium, Sunday Agbo, da abokin burminsa Eucharia Ogwale.

Sauran wadanda rundunar ta sanar da kamawa sun hada da tsohon sakataren yada labaran gwamna, Emmanuel Uzor, wanda yanzu mai bawa gwamna shawara ne da kuma wani hadimin gwamna mai suna Emmanuel Igwe.

Tsohon dan majalisar dokoki na karamar hukumar Ohaukwu da kuma Frank Owe, mai bawa gwamna shawara a kan cigaban matasa na daga cikin wadanda rundunar 'yan sandan ta kama.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an kama dukkan masu rike da mukaman ne bisa umarnin, Kelechi Igwe, mataimakin gwamman jihar Ebonyi.

Kwamishinan 'yan sandan Ebonyi ya kama hadiman gwamnan jihar biyu da shugaban karamar hukuma
Kwamishinan 'yan sandan Ebonyi ya kama hadiman gwamnan jihar biyu da shugaban karamar hukuma
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan ya gayyaci masu rike da mukaman siyasa da kuma masu ruwa da tsaki daga yankin zuwa wurin taron gaggawa da ya kira a gidan gwamnati biyo bayan rikicin da aka a yankin a ranakun Juma'a da Asabar.

Igwe ya gayyaci kwamishinan 'yan sanda da sakataren gwamnatin Ebonyi da alkalin alkalan jihar da kuma kwamishinan kananan hukumomi zuwa wurin taron da aka fara da misalin karfe 9:00 na safe.

Sai dai, sa'a daya da fara taron, sai ga manyan motocin 'yan sanda guda goma sun shigo tare da yi wa wurin taron kawanya kafin daga bisani kwamishinan ya shiga wuri taro ya fito da mutanen tare da tafiya da su.

A ranar Asabar ne rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da wasu tara suka samu raunuka sakamakon rikicin da ya barke a yankin a tsakanin kabilun Effrum mazauna kori da mazauna Ezra.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel