NCoS: Mrabure ya zama shugaban riko bayan ritayar Ja'afaru

NCoS: Mrabure ya zama shugaban riko bayan ritayar Ja'afaru

- Duk da samun karin tsayin wa'adi har sau biyu a baya, shugaban hukumar NCoS da ke kula da gidajen yari na kasa ya yi ritaya

- Wa'adin tsohon shugaban NCoS ya kare tun a cikin watan Yuli na shekarar 2019, amma sai shugaba Buhari ya kara masa wa'adin shekara

- Bayan karewar shekarar ne sai ministan harkokin cikin gida ya sake karawa tsohon shugaban watanni shidda

Babban mataimakin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali (NCoS), DCG John Mrabure, ya zama sabon shugaban riko na hukumar.

Kafin sanar da nadinsa a matsayin shugaban riko, Mrabure ya kasance DCG mai kula da ma'aikatan hukumar NCoS.

Mrabure yana cikin manyan jami'an NCoS guda goma da shugaba Buhari ya amince da kara musu girma a cikin watan Yuli na shekarar 2019.

PRNigeria ta rawaito cewa Mrabure ya karbi aiki daga hannun tsohon shugaban hukumar NCoS, Ja'afaru Ahmed, wanda ya yi ritaya bayan karewar wa'adin zangon mulkinsa da aka kara masa har sau biyu a baya.

NCoS: Mrabure ya zama shugaban riko bayan ritayar Ja'afaru
NCoS: Mrabure ya zama shugaban riko bayan ritayar Ja'afaru
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ne ya fara karawa Ja'afaru tsawon wa'adin mulkinsa bayan ya kare a ranar 21 ga watan Yuli a shekarar 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu gagarumin cigaba a aiyukan hukumar NCoS a karkashin jagorancin Ja'afaru.

Minista Aregbesola ne ya amince da nadin Mrabure a yayin da aka tsayar da ranar 21 ga watan Janairu domin bikin bankwana da Ja'afaru a hedikwatar NCoS da ke Abuja.

Daga bisani, Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya sake karawa Ja'afaru watanni shidda bayan karewar shekara daya da Buhari ya kara masa.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.

Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng