Shi muke kwaikwayo; Gwamna Badaru ya jinjinawa tsohon gwamna Sule Lamido

Shi muke kwaikwayo; Gwamna Badaru ya jinjinawa tsohon gwamna Sule Lamido

- Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, ya jinjinawa tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido

- A cewar Badaru, gwamnatinsa ta kwaikwaya tare da cigaba da aiyukan raya kasa da gwamnatin Lamido ta fara

- Wannan shine karo na farko da aka ji Badaru na yabon Lamido a gaban taron jama'a da manema labarai

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya jinjinawa tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, bisa gina tituna da sauran aiyukan raya kasa da ya yi a jihar lokacin ya na kan mulki.

Gwamnan ya yi wannan yabo ne lokacin da ya ke ƙaddamar da gina titin da ya tashi daga Dutse zuwa Birnin Kudu wanda aka gina akan kuɗi Naira Biliyan N7.7, kamar yadda Tribune ta rawaito.

Badaru, dan jam'iyyar APC, ya ce tsohon gwamna Lamido, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi namijin kokari wajen gina manyan tituna a jihar.

A cewar gwamna Badaru, "A wurinsu muka gani, muka kwaikwaye daga wurinsu, muka cigaba da yi tare da dorawa daga inda suka tsaya."

Shi muke kwaikwayo; Gwamna Badaru ya jinjinawa tsohon gwamna Sule Lamido
Shi muke kwaikwayo; Gwamna Badaru ya jinjinawa tsohon gwamna Sule Lamido @Lindaikejiblog
Source: Twitter

Ya kara da cewa, "Tun farkon wannan gwamnati, mun yi aikin gina tituna da tsawon su ya kai kilomita 1550. Wannan ya haɗa da titunan da gwamnatin baya ta faro da kuma wanda mu ka fara"

Gwamnan ya yi bayanin cewa cigaba da gina tituna da suka gada daga gwamnatin baya tare da gina wasu sabbi, babban cigaba ne ga jama'ar jihar ta Jigawa.

Tituna biyu da gwamnan ya ƙaddamar sun hada da Dutse zuwa Dangwali mai tsawon kilomita 35.7 an kuɗi biliyan 4.643 da kuma wanda ya tashi daga Madobi zuwa Baranda kilomita 16.8 kan kuɗi biliyan 3.194.

A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa hukumar kula da harkar lafiya a matakin farko; NPHCD ta sanar da cewa nan bada dadewa za'a fara rabawa jihohi alluran rigakafi tare da bayyana adadin da kowacce jiha za ta samu.

Gwamnatin tarayya ta ce zata yi la'akari da alkaluman masu kamuwa da cutar wajen rabon alluran rigakafin.

A cewar NPHCD, Jihar Kano za ta samu alluran rigakafi mafi yawa, 3,557, a rukunin farko na rabon.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel