Fittatun Farfesoshin Nigeria 13 da suka rasu a 2020 (Hotuna)

Fittatun Farfesoshin Nigeria 13 da suka rasu a 2020 (Hotuna)

Shekarar 2020 ta kasance shekara mai muni a fadin duniya musamman yadda annobar korona ta gigita tattalin arzikin duniya, har ta kai tattalin arzikin wasu kasashe ya durkushe ga baki daya.

Wannan ya janyo nakasu a rayuwar mutane fiye da ko yaushe.

Bangaren ilimi shima ya fuskanci cikas a cikin shekarar, da yawan furofesoshi sun kwanta dama.

A kasa jerin wasu manyan furofesoshin Najeriya ne da suka rasu a 2020, kamar yadda Daily Trust ta tattara.

1. Jerry Agada

Prof. Jerry Agada, wanda ya mutu cikin watan Disambar 2020, ya na da shekaru 68 bayan yar gajeruwar jinya, tsohon mimistan ilimi ne kuma, shugaban hukumar ma'aikata ta jihar Benue.

An haifi Agada a watan Nuwamba, 1952 a karamar hukumar Orokan da ke jihar Benue.

An nada shi babban sakataren hukumar shirya jarrabawar jihar Benue a shekarar 1996.

A shekarar 1999 ya ɗaga zuwa matakin sakataren din-din-din, a ma'aikatar yada labarai, matasa, wasanni da kuma al'ada.

2. Shehu Bida

Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna)
Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna). Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Farfesa na farko a bangaren karatun likitan dabbobi daga arewacin Najeriya kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bida, sannan farfesa na farko a kasar Nupe, Shehu Jibrin, farfesa na farko dan kasar Nupe kuma farfesa na farko likitan dabbobi a arewacin Najeriya, ya rasu cikin watan Nuwamba ya na da shekaru 86.

An nada shi kwamishinan kasuwanci, masana'antu da zuba hannun jari.

A sakon ta'aziyyar da gwamna Abubakar Sani Bello ya aikewa iyalansa yace "Professor Bida ya yi rayuwa mai kyau kuma ya bar abin da za a dinga tuna shi."

3. Femi Odekunle

Prof. Femi Odekunle shine farfesa na farko a bangaren nazarin laifufuka wato Criminology a Najeriya.

Ya rasu sanadiyar COVID-19 cikin watan Disamba kuma har zuwa lokacin da ya rasu mamba ne a kwamitin bada shawarwari kan yaki da cin hanci da rashawa, PACAC.

Ya kuma taba rike mukamin mai bada shawara ga shugaban ma'aikata, Gen. Oladipo Diya lokacin mulkin Gen. Sani Abacha.

4. Habu Galadima

Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna)
Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna). Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Prof. Habu Galadima, DG, NIPSS, Prof. Habu Galadima tsohon babban daraktan NIPSS ya rasu a Disambar 2020.

An haife shi a 1963 a karamar hukumar Toto da ke jihar Nasarawa, Galadima ya karanta kimiyyar siyasa a jam'i ar Jihar Plateau, da ke Jos.

Yayi digirin sa na biyu a 1990 sai PhD a shekarar 2006 duk daga jam'i ar.

Galadima ya zama farfesa a sashen kimiyyar siyasa a 2009.

Ya rike mukamin shugaban sashen da kuma mataimakin shugaban tsare tsare na makarantar.

Galadima ya yi aiki a bangarori daban daban irin DFID, ECOWAS, bankin duniya da kuma UNDP.

5. Ayobami Akinwale

Prof. Ayobami Akinwale, wanda ya shahara a fina finan shekarun 1990 Sango, ya rasu a Satumbar 2020.

Akinwale shine shugaban zane da al'ada na jihar Oyo kuma shugaban sashen al'ada na jamiar Ilorin.

Ma'abota kallon fina finai zasu ci gaba da tuna Akinwale, wanda ya taba lashe kyautar African Movie Academy Award (AMAA), na tsohon jarumi kuma daya daga cikin kwararru a harkar a fina finan sa kamar Sango (1997),Ladeepo Omo Adanwo (2005), Isense Aje da wasu da dama

6. Lovett Lawson

Prof. Lovet Lawson, wanda ya kammala jami'ar jihar Lagos a 1957 ya kuma samu PhD din sa a jami'ar Liverpool, ya mutu sanadiyyar annobar Corona a 2020.

Farfesan cutukan da ake iya kamuwa da su shi ne mataimakin ciyaman, shugabannin Zankil Medical Centre, Abuja.

7. Aliyu Dikko

Tsohon farfesan Physiology, prof. Aliyu Dikko malami ne a sashen Human physiology, na makarantar koyon likitanci, jami'ar Bayero, Kano.

Dikko ne tsohon shugaban makarantar.

Dikko ya rasu a watan Afrilu, 2020, kuma ya taimaka an bude sassan lafiya uku a jami'ar Bayero, jami'ar jihar Kaduna da kuma jami'ar Yusuf maitama sule, Kano.

8. Alaba Adenuga

Prof. Alaba Adenuga shi ne tsohon shugaban sashen ilimi, jami'ar Olabisi Onabanjo, jihar Ogun.

Har zuwa lokacin da ya rasu shine shugaban hukumar tsaron jami'ar kuma shugaban tawagar manyan malamai.

9. Ali Muhammad Garba

Prof. Ali Muhammad Garba farfesan kasuwanci ne a jami'ar Bayero, Kano.

Ya mutu cikin watan Disamba bayan gajeriyar jinya, inji iyalan sa.

Har ya mutu, Prof Garba yana koyarwa a sashen kasuwanci da kuma Dangote Business School, duk a jami'ar Bayero.

10. Balarabe Maikaba

Prof. Balarabe Maikaba babban malami ne kuma tsohon HOD, sashen koyon aikin jarida, jami'ar Bayero Kano.

Maikaba ya rasu bayan gajeriyar jinya a wani asibiti mai zaman kansa ana tsaka da Corona a jihar.

Maikaba ya gama makarantar a 1991, kuma ya samu aiki anan har ya zama farfesa a Oktoba 2018.

11. Haruna Wakili

Prof. Haruna wakili da daliban sa kewa kirari da "a gentle extraordinaire" ya rasu a watan Yuni 2020.

Tsohon kwamishinan ilimi a jihar Jigawa malami ne da tarihi ba zai manta ba.

Shine tsohon shugaban Aminu Kano Centre for democraric training and research, gidan Mumbayya, sahalewar jami'ar Bayero Kano.

12. Ibrahim Ayagi

Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna)
Fittatun farfesoshin Nigerian 13 da suka mutu a 2020 (Hotuna). Hoto: daily_trust
Asali: Twitter

Marigayi Ibrahim Ayagi tsohon dalibin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ne.

Farfesan masanin tattalin arziki ne da ya halarci jami'ar Pittsburg, Pennsylvania, a Amurka.

Yayi kwamishinan ilimi a jihar Kano kuma shi ya kafa makarantun kimayya na Dawakin Tofa da Dawakin Kudu.

13. Oladipo Akinkugbe

Prof. Oladipo Akinkugbe, sannanen farfesan likitanci a jami'ar Ibadan ya rasu a Yunin 2020, ya na da shekaru 86.

Akinkugbe, wanda ya yi likita tsawon shekara 60, shi ne shugaban asibitin jami'ar ibadan.

Ya taba rike shugabancin hukumar JAMB.

Ya taba zama uban jami'ar Ahmadu Bello, da ke Zaria kuma tsohon shugaban sashen likitanci, jami'ar Ibadan.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel