An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku

An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku

- Tsohon kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Metuh, ya bar gidan yarin Kuje bayan ya shafe watanni goma

- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Metuh a gaban kotu bisa zarginsa da karbar miliyan 400 daga ofishin Dasuki ta haramtacciyar hanya

Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, ya shaki iskar 'yanci bayan ya shafe watanni goma a gidan yari.

Gidan talabijin na Channels ya nuna hotunan Metuh yayin da ya ke barin gidan yari na Kuje a Abuja, babban birnin tarayya.

Channels ta bayyana cewa jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ne ya fara wallafa hotunan Metuh na barin gidan yari a shafinsa na tuwita.

Fayose ya taya Metuh murnar samun 'yanci inda ya bayyana cewa, "barka da dawowa gida Olisa Metuh, komai tsananin wuya, sauki na biye da ita....."

An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku
An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku @Channels
Asali: Twitter

KARANTA: An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano

An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku
An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku @Channels
Asali: Twitter

An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku
An saki tsohon kakakin jam'iyyar PDP bayan wata 10 a kurkuku @Channels
Asali: Twitter

Hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci, ita ce ta fara gurfanar da Metuh tare da wani kamfani, Destra Investment Limited a gaban mai shari'a Jastis Okon Abang na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Ana tuhumar Metuh da laifin karbar kudi har miliyan dari hudu ta haramtacciyar hanya daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a harkar tsaro (NSA), Kanal Sambo Dasuki.

KARANTA: Sojoji sun sheke 'yan fashi uku a daura da sansanin NYSC da ke Mangu, sun kwaci bindigu

A ranar 25 ga watan Fabarairu na shekarar 2020 ne mai shari'a Abang ya zartar da hukuncin daurin shekaru bakwai ga Metuh.

Metuh ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun da ke kasanta ta yanke masa.

Watanni goma bayan daukaka karar, kotun koli ta amince da dalilan Metuh tare da warware hukuncin da kotun farko ta zartar da kuma bayar da umarni a sake shigar da sabuwar kara a kansa.

An saki Metuh daga gidan yarin Kuje sati daya bayan kotun koli ta warware hukuncin kotun farko.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, ya ce sai mutanen yankin kudu maso gabashin kasar nan, na 'yan kabilar Igbo, sun sauya halayyarsu kafin su samu takarar kujerar shugaban kasa.

Sanata Anyim, ya yi wannan iƙirari ne a wani biki mai taken World Igbo Summit, wanda jami'ar Gregory dake Uturu a jihar Abia ta shirya a karo na shida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Cikin bayaninsa mai taken, "Duban tsanaki kan buƙatar ƙabilar Igbo ga mulkin ƙasar nan tare da tsarin cimma hakan," Anyim ya nuna giɓin dake akwai na ɓallewa ko sauya tsarin fasalin ƙasar nan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel