Jagoran kasar Iran ya yiwa Amurka isgili kan halin da ta shiga na rudanin zaben 2020
Jagoran kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yiwa halin rudanin da Amurka ta shiga yayin zaben shugaban kasar dake gudana yanzu haka.
Ayatollah ya ce zaben nan ya tonawa Amurka asiri kan ainihin yadda demokradiyyansu take.
Sama da sa'o'i 24 bayan kammala kada kuri'u a jihar Alaska, har yanzu ba'a san wanda zai yi nasara a zaben ba.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jefa rudani cikin al'ummarsa yayinda ya fara zargin magudi cikin zaben, yayinda abokin hamayyarsa, Joe Biden, ya tuhumci Trump da kokarin dakatad da kirgan kuri'u.
"Ikon Allah! Idan wani yace wannan ne zabe mafi muni da cuta a tarihin Amurka. Za'a ce wa ya fadi hakan? Shugaban kasan da ke kai yanzu," Ayatollah Khamenei yace.
"Yayinda abokin hamayyarsa ke cewa Trump na niyyar magudin zabe! Haka fa zaben Amurka da Demokradiyyarta take"

Asali: UGC
Amurka ta fuskanci matsanancin rabuwan kan al'ummarta tun lokacin da Trump ya fito takaran shugaban kasa shekaru baya.
Duk da zargin da Amurka ke yiwa Iran cewa tana kokarin amfani da dandalin soshiyal midiya wajen yi mata kutse, shugaban Iran ya bayyana cewa babu ruwanta da wanda zai yi nasara.
Asali: Legit.ng