Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi

Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi

- Wasu matasa sun fara zanga-zanga a akalla jihohin Amurka uku

- Har yanzu ba'a san wanda zai lashe zaben yayinda yake sauraron sakamakon zabe a jihohi 7

- Trump ya ce shi ya lashe zabe amma ana kokarin yi masa magudi

An fara zanga-zanga a wasu jihohin Amurka yayinda sakamakon zabe ke cigaba da fitowa kuma har yanzu ba'a san wanda zai yi nasara ba, The Cable ta tattaro.

A birnin Los Angeles, yan sanda sun damke masu zanga-zanga 40 bayan sun toshe layin dogon jirgin kasa.

Hukumar yan sandan Los Angeles LAPD ta sanar ta shafinta na Tuwita cewa "Sakamakon wani taron jama'a maras tsari, LAPD na sanarwa jama'a kada su taru a 18th Street da Figuroa."

"A daidai wannan lokaci, duk wanda ke wajen ya watse yanzu kuma ya bi umurnin yan sandan."

Daga baya LAPD ta sanar da ganin mutane 30 a wajen, yayinda aka "damke kimanin mutane 40 da laifin toshe layin dogon jirgin kasa kuma suka ki watsewa."

A Seattle, birnin Washington DC, Fox News ta ruwaito cewa an damke akalla mutane takwas suna zanga-zanga.

Wadanda aka damke sun hada "masu zuba kutsoshi a kan titi."

Hakazalika a biranen Raleigh, Oregon da Minnesota, an samu rahotannin zanga-zanga.

Har yanzu akwai kishin-kishin rikici yayinda sauran sakamako ke shigowa musamman wadanda aka kada ta akwatin sako.

KU KARANTA: Baka isa ka hana karasa kirgan kuri'u ba - Abokin hamayyar Trump ya yi masa raddi kan maganar zuwa kotu

Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi
Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi Hoto: VOA
Asali: UGC

Trump yayi alfaharin cewa lallai ya lashe wannan zaben sai dai idan aka danne masa.

"Muna son a daina kada kuri'u," Trump yace, yana nufin a daina kirgan kuri'un da aka turo ta akwatin sako.

Jihohin da suka rage ana sauraron sakamako sune Georgia, Michigan, Pennsylvania, Wisconsin, da Nevada.

A yanzu haka Joe Biden na jam'iyyar Democrat na kan gaba da makin Electoral College 238 yayinda Trump na Republican na biye da shi da makin Electoral College 213, bisa alkaluman kafofin yada labaran Amurka.

Wanda ya riga kai wa 270 ne ya lashe zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel