Baka isa ka hana karasa kirgan kuri'u ba - Abokin hamayyar Trump ya yi masa raddi kan maganar zuwa kotu

Baka isa ka hana karasa kirgan kuri'u ba - Abokin hamayyar Trump ya yi masa raddi kan maganar zuwa kotu

- Abokin hamayyar Donald Trump ya mayar masa da martani kan jawabin da yayi

- Trump ya bukaci a tsagaita kirgan kuri'un jama'an da suka kada a jihohin da suka rage

- Ya lashi takobin zuwa kotu bayan zaben

Kwamitin yakin neman zaben dan takara Joe Biden ta caccaki shugaba Trump bisa barazanar da yayi na hana cigaba da kirgan kuri'u mutane da suka kada a jihohin da suka rage musamman Pensylvannia.

Kwamitin ta ce wannan abu da Trump ke barazanar yi ya sabawa hankali.

"Jawabin shugaban kasa na daren nan na kokarin hana cigaba da kirgan kuri'u ya sabawa hankali kuma bai dace ba," Diraktan yakin neman zaben Biden, Jen O'Malley yace.

"Bai taba faruwa a tarihin kasar mu ba a ce shugaban kasan Amurka zai dannewa mutan Amurka muryarsu a zaben kasa."

"Muna da lauyoyi dake kasa da muka yi niyyar amfani... kuma za suyi nasara," ya kara.

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 213, Biden 238

Baka isa ka hana karasa kirgan kuri'u ba - Abokin hamayyar Trump ya yi masa raddi kan maganar zuwa kotu
Baka isa ka hana karasa kirgan kuri'u ba - Abokin hamayyar Trump ya yi masa raddi kan maganar zuwa kotu
Asali: UGC

Wannan jawabi ya biyo bayan maganar da Trump yayi na cewa lallai ya lashe wannan zaben.

"Muna son a daina kada kuri'u," Trump yace, yana nufin a daina kirgan kuri'un da aka turo ta akwatin sako.

Jihohin da suka rage ana sauraron sakamako sune Georgia, Michigan, Pennsylvania, Wisconsin, da Nevada.

A yanzu haka Joe Biden na jam'iyyar Democrat na kan gaba da makin Electoral College 238 yayinda Trump na Republican na biye da shi da makin Electoral College 213, bisa alkaluman kafofin yada labaran Amurka.

Wanda ya riga kai wa 270 ne ya lashe zabe.

Mun kawo muku cewa shugaba Donald Trump a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa ya lashe zaben kujerar shugaban kasa, duk da cewa ba'a kammala fitar da sakamako ba, kamar yadda muka gano a bidiyon Aljazeera.

Hakazalika Trump ya lashi takobin garzayawa kotun koli domin dakatad da kirgan sauran kuri'u.

"Mun lashe zaben," Trump yace a jawabin da yayi da safiyar Laraba a fadar White House.

"Domin alherin kasar nan, wannan lokaci ne mai muhimmanci. Wannan magudi ne babba a kasarmu. Muna son ayi amfani da doka yadda ya kamata. Saboda haka, zamu garzaya kotun koli," Trump ya kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel