Wawusan kayan tallafin Korona: Wannan zalunci ne, bai hallata ba - Sarkin Musulmi

Wawusan kayan tallafin Korona: Wannan zalunci ne, bai hallata ba - Sarkin Musulmi

- Sarki Musulmi ya yi Alla-wadai da irin sace-sacen kayan abincin da aka yi a Najeriya

- Sultan ya ce ya zama wajibi masu fada aji su fito suyi magana kan lamarin

- Ya yabawa matasan arewa bisa rashin biyewa sauran mutane wajen yin hakan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya siffanta wawusan kayan tallafi, sace-sace da lalata ma'aikatun gwamnati a matsayin zalunci da mugunta

Sarkin wanda yayi jawabi a taron murnar cikar Arewa House shekaru 50, ya jinjinawa matasan Arewa bisa biyayyan da suka yiwa shugabanni, rahoton Daily Trust.

Ya ce talauci ba uzuri bane da zai sa a rika lalata dukiyoyin kasa.

Yace: "Mun san akwai talauci amma talauci ba uzuri bane na yin mugunta."

"Saboda abinda ya faru a kwanakin nan mugunta wasu bata gari sukayi kuma ina ganin akwai bukatar muyi Alla-wadai da hakan."

Ya kalubalanci shugabannin Arewa suyi aiki wajen gina yankin domin wanzar da manufar marigayi Sir Ahmadu Bello.

KU KARANTA: Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna

Wawusan kayan tallafin Korona: Wannan zalunci ne, bai hallata ba - Sarkin Musulmi
Wawusan kayan tallafin Korona: Wannan zalunci ne, bai hallata ba - Sarkin Musulmi Credit: Presidency
Asali: Twitter

A wani labari daban, Mai Martaba Obong na Calabar, Edidem Ekpo Okon Abasi Otu, ya daura laifin sace-sace da fashe-fashen da akayi a jihar Cross River makon da ya gabata kan gwamna Ben Ayade, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira ga gwamnan ya sauka daga mulki domin baiwa gwamnatin rikon kwarya daman gyara kuma ya natsu ya dauki darasin yadda ake mulki da tafiyar da al'umma.

Sarkin wanda yayi jawabin lokacin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar, Liyel Imoke, ya ce an kai hare-haren ne saboda gwamnan ya daina shirya zaman hukumomin tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel