Muna tsoron fitowa cikin gari yanzu - Jami'an yan sanda

Muna tsoron fitowa cikin gari yanzu - Jami'an yan sanda

- Bata gari na yi wa iyalanmu da mu kanmu bara zana - Jami'an yan sanda

- Mun rasa yan sanda 23, an kona mana wurare 205 - Sifeto Janar

- Ban taba gani wani abu irin wannan ba, ban yi tunanin zan rayu ba - Wani dan sanda

Jami'an yan sanda sun janye daga tituna domin gudun sake fuskantar masu zanga-zanga yayinda bata gari masu muggan makamai suke cin karnukansu babbaka suna sace-sace da kone-kone.

Gano runbun tallafin COVID-19 da ya kamata a rabawa mutane a Legas ya kara bude idanuwan mutane a fadin tarayya inda kowa ya fara fasa na jiharsa ana sace kayan abincin.

Sace-sacen da lalace-lalacen ya kai wasu na kona allon ma'aikatun gwamnati da kuma sace taraktoci.

Manyan wadanda wannan abin ya shafa sune jami'an yan sandaN Najeriya da hukumar.

Muna tsoron fitowa cikin gari yanzu - Jami'an yan sanda
Muna tsoron fitowa cikin gari yanzu - Jami'an yan sanda Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yaudararmu kayi muka zabeka - Dattawan Jihar Neja ga Buhari

Duk da umurnin da Sifeto Janar ya baiwa jami'ansa su koma bakin aiki, yan sanda a fadin tarayya sun ki bin umurninsa, cewar rahoton Vanguard.

Galibin yan sandan sun ki komawa bakin aiki suna tsoron bayyana cikin jama'a saboda tsoron kada a far musu kuma saboda yan batagari na yiwa iyalansu barazana.

Kadan daga cikin yan sandan da sukayi karfin halin zuwa aiki na boye kayan sarkinsu cikin jaka har sai sun isa ofis kafin su sanya gudun kada a afka musu.

A jawabin IGP Mohammed Adamu, ya ce yan sanda 23 aka kashe lokacin rikicin yayinda aka kona wurare 205.

DUBA NAN: Yan bindiga sun hallaka Maigari, Soja da wasu mutane 18 a jihar Katsina

IGP, Mohammed Adamu a ranar Juma'a ya faɗa wa jami'an rundunar su kare kansu idan aka kai musu hari a gari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƴan sandan ya yi jawabi ne a hedkwatar rundunar da ke Abuja bayan ziyarar zagaye da ya yi don ƙarfafawa gwiwar jami'an da wasunsu sun dena fita tituna.

Adamu ya kuma ce masu zanga-zangar EndSARs sunyi yunkurin rage wa ƴan sandan ƙwarin gwiwa amma rundunar za ta fito da tsarin tallafawa wadanda suka rasa rayukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel