Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 13 a mako daya a Borno - DHQ

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 13 a mako daya a Borno - DHQ

- Rundunar sojiji ta Operation Lafiya Dole, ta samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 13 tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 29, da kuma kwace makamai a hannunsu

- Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin da yake bayar da jawabin sati a kan harkar tsaron arewa maso gabas a Abuja

- Ya sanar da nasarar da rundunar suka yi ta mayar da harin da 'yan Boko suka kai Mallam Fatori, Ngwuri Gana da Jamacheri da ke Borno

Hedkwatar tsaro tace rundunar Operation Lafiya Dole ta ragargaji 'yan Boko Haram 13 tsakanin 22 ga watan Oktoba zuwa 29, Daily Nigerian ta wallafa.

Kakakin rundunar, John Enenche ya sanar da hakan ranar Juma'a, yayin da yake bayar da jawabi karshen mako a Abuja a kan arewa maso gabas.

Enenche ya ce sojojin rundunar OPLD na sama da kasa sun yi ayyuka da dama a cikin makonnan.

Ya ce rundunar ta kai wa 'yan bindigan hari a maboyarsu, sun kuma mayar da harin da 'yan bindigan suka kai musu sannan sun samar da tsaro ga 'yan gudun hijira.

A cewarsa, jagoran rundunar ya samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda da dama, sannan sun samu nasarar kashe sauran 'yan ta'addan guda 13 a garin Mallam Fatori, Ngwuri Gana da Jumacheri da ke Borno.

Sun kuma samu nasarar kwace wasu abubuwa masu fashewa, IEDS da bindigogi 2 daga hannun 'yan ta'addan.

Rundunar ta samu nasarar mayar da hari 3 da 'yan Boko Haram suka kai musu a Magumeri, Gajiram da Damboa da ke Borno.

Ya kara da cewa, "A wannan karon battan, rundunar ta samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 13 da kwace miyagun makamai daga hannunsu. Gabadaya 'yan ta'adda 22 kenan aka kashe a Damboa."

KU KARANTA: Hotunan katafaren sabon gidan Aubameyang da ya mallaka a birnin London

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 13 a mako daya a Borno - DHQ
Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 13 a mako daya a Borno - DHQ. Hoto daga @DailyNigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fara kama masu magaungunan gargajiya da suke amfani da kalamen batsa wurin tallar magungunansu, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kirkiri wani kwamiti da ke karkashin kwamishinan lafiya, Dr Ibrahim Tsanyawa, KAROTA, Hisbah da sauran jami'an tsaro a matsayin 'yan kwamitin.

Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba, inda yace an gama duk wasu shirye-shirye don fara ayyuka a kwamitin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel