Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

- Bayan fursunoni da dama sun tsere daga gidajen gyaran hali da ke Oko da Benin lokacin zanga-zangar EndSARS

- 'Yan sanda sun kara kama daya daga cikin fursinan sakamakon laifin kisa da ya aikata

- Dama 'yan sandan sun kama wasu 10 daga cikin fursinonin sun yi fashi da makamai, wasu kuma kisa

'Yan sanda sun samu nasarar damkar daya daga cikin fursinoni 1,993 da suka gudu daga gidan gyaran halin Oko da Benin, sakamakon kashe wani da yayi.

The Cable ta ruwaito yadda fursinoni suka gudu sakamakon rikicin zanga-zangar EndSARS.

Yayin da suka jera wadanda ake zargin masu laifi ne guda 126 a ranar Laraba, Babatunde Kokumo, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce 10 daga cikinsu fursinoni ne da suka tsere.

Ya ce 'yan sanda sun samu nasarar kara damkar fursunonin da suka koma aikata laifuka.

KU KARANTA: Gadon sarauta: Rikici ya barke, an sace basaraken rikon kwarya tare da cin zarafinsa

Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu
Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa, "Mun zage damtse wurin neman masu laifi. Kuma ina so kusan cewa yanzu haka mun samu nasarar damkar 10 daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyara halin Oko da na Benin.

"Daya daga cikin fursunonin gidan gyara halin Oko, ya koma kauyensu a ranar don kashe wanda yayi shaidarsa a laifin da ya kai shi ga shiga gidan gyaran halin.

"Wasu 3 daga cikinsu kuma sun je yin kwacen wata mota kirar Lexus, yayin da 'yan sanda suka damkesu."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama 'yan gidan fursuna da suka tsere da laifin fashi da makami

A cewarsa, "Wasu biyu sun sace wata mota kirar Toyota. Kuma dama a gidan gyaran halin suka hadu. Rundunar 'yan sanda da ke Okada, jihar Edo ne suka kama su. Yanzu haka su 10 kenan aka kama.

"An samu nasarar amsar bindigogi daga hannun 'yan ta'addan."

A wani labari na daban, a taron da FEC tayi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya amince da biyan Naira Biliyan 4.5 don samar da takardun jarabawa da kuma gyaran titinan da ke kauyakun babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanarwa manema labaran cikin gidan gwamnati, tare da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad, inda yace an ware Naira biliyan 2.9 don samar da kayan jarabawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel