Buhari ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya yayin Maulidi

Buhari ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya yayin Maulidi

- Shugaban kasar najerya, Muhammadu Buhari ya aike da muhimmin sakon Maulidi ga 'yan kasa

- Ya yi kira ga 'yan Najerya da su rungumi hakuri, juriya da kuma kaunar juna a zukatansu

- Kamar yadda yace, lokaci yayi da za su ajiye makamansu domin tabbatar hadin kai

Yayin da musulman Najeriya za su taru da sauran musulman duniya wurin farin cikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW).

Su nuna kauna da fahimta ga al'umma, da kuma bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa, Premium Times.

A wani sako da shugaban kasa ya tura wa musulmai a kan maulidin fiyayyen halitta, wacce ta zama ranar hutu a Najeriya, shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya musamman matasa da su bar duk wani mummunan kudiri a kan zanga-zangar da ke jawo sace-sace da lalata dukiyoyin gwamnati da na al'umma.

Buhari ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya yayin Maulidi
Buhari ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya yayin Maulidi. Hoto daga @Premimutimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanwo-Olu ya fusata da rikicin kabilanci, ya yi tsokaci mai zafi

Ya kuma tabbatar da cika alkawarinsa na yin adalci ga duk wanda jami'in 'yan sanda suka zalinta.

Shugaban kasa ya kara da rokar 'yan Najeriya da tabbatar da sun kiyaye matakan kula daga kamuwa da cutar COVID-19, duk da ganin an kusa kawo karshenshi a Najeriya.

"Ganin yadda guguwar COVID-19 ta kara tashi a wasu kasashe, ya kamata a jirace ta a nan. Mu tabbatar yadda aka samu cutar tayi kasa, ba'a jawo dalilin sata tayi sama ba. Don tattalin arzikinmu yayi can kasa," a cewarsa.

Don haka ne shugaban kasa ya shawarci duk 'yan Najeriya da su kiyaye dokokin kamuwa daga cutar COVID-19, kamar wanke hannaye, saka takunkumi da dokar nesa-nesa da juna.

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

A wani labari na daban, a taron da FEC tayi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya amince da biyan Naira Biliyan 4.5 don samar da takardun jarabawa da kuma gyaran titinan da ke kauyakun babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanarwa manema labaran cikin gidan gwamnati, tare da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad, inda yace an ware Naira biliyan 2.9 don samar da kayan jarabawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel