Jerin sunayensu: Mu na gina filayen saukar jirgi a jihohi 10 - FG

Jerin sunayensu: Mu na gina filayen saukar jirgi a jihohi 10 - FG

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa tana da shiri mai karfi na bukasa harkar sufurin jiragen sama

- Hadi Sirika, ministan sufurin jirage, ya ce gwamnatin tarayya ta na gina sabbin fiayen jirage 10

- Ana gina filayen jiragen ne a wasu jihohin Najeriya 10 da basu da filin jirgi a baya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa tana gina sabbin filayen jiragen sama har guda 10 a faɗin ƙasar nan don bunƙasa harkar sufurin jiragen sama.

Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Sanatoci na harkar sufurin jirage.

Ya bayyana haka ne yayin da yake kare kasafin kuɗin Ma'aikatar harkokin sufuri da hukumomin da ke karkashinta.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

Hakan ya zo dai-dai lokacin da sanatoci ke alhinin lalatacewar kayan aiki a filin jirgin sama na Minna, Zuru da kuma Ajaokuta.

Tun daga shekarar 2015 lokacin da gwamnati mai ci ta karɓi ragamar mulki ake samun cigaba mai kyau ta hanyar kirkirar sabbin hanyoyi da ake amfami da su don kawowa kasa cigaba, a cewar ministan.

Jerin sunayensu: Mu na gina filayen saukar jirgi a jihohi 10 - FG
Sanata Hadi Sirika @TheCable
Asali: Twitter

Ministan ya ƙara da cewa ɓangaren sufurin jiragen sama yafi kowanne ɓangare samun cigaban tattalin arziƙi.

A cewarsa, gwamnati na da niyyar gina sabbin filayen jiragen sama a jihohin Anambra, Benue, Ekiti, Nasarwa, Ebonyi, Gombe, da sauran wasu jihohi.

Ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta karɓi ragamar Filayen jiragen sama na Kebbi, Osubi, da Dutse.

''Jihar Gombe sun yi roƙo a rubuce ga hukumomin gwanmatin tarayya akan su karɓi ragamar filin jirgin saman jihar.

"Mun shaida yadda harkar sufurin jiragen sama ta samu haɓaka a shekarar 2018 inda ta kasance ɓangare na biyu da yafi kowanne samun ɓunƙasar tattalin arziƙi a shekarar 2019.

''Harkar sufurin jiragen sama itace mafi sauri wajen ɓunƙasar tattalin arziƙin kasa, baya ga haka ta bawa ƙasa gudunmawar bunkasar tattalin arziki a cikin gida (GDP).

''Daga shekarar 2015 an samu gagarumin cigaba a harkar sufurin jiragen sama, an samu ƙarin filayen jiragen sama.

''Yanzu haka an samu ƙarin filayen jirgin sama aƙalla guda bakwai(7). Wasu an kammalasu, wasu kuma ana kan gudanar da ayyukan su.

KARANTA: Tsallake rijiya da baya: An kwaci babban Sarki da kyar bayan batagarin matasa sun kutsa kai fada

"Akwai filayen jirgin sama masu zuwa nan bada dadewa ba a Benue, Ebonyi, Ekiti, Lafia, Damaturu, Anambra da sauransu.

"Hakan na nuni da cigaban da aka samu a harkar sufurin jirgin sama a wannan gwamnatin.

"Muna da akalla sabbin filayen jiragen sama guda goma da ke nan tafe, wannan kusan rabin filayen jiragen saman da muke dashi ne a Najeriya.

''Muna ƙoƙarin ganin an samu ƙarin kaso hamsin na adadin filayen jiragen saman da muke dasu," a cewar Sirika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel