Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3

Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3

- Babbar kotun Kubwa da ke birnin Abuja, ta umarci Abubakar Atiku da yayi gaggawar mayar wa tsohuwar matarsa yaransu 3

- Abubakar Atiku, da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, dama ya kwace yaran 3 ne tun bayan rabuwarsu

- Alkali Mai shari'a, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai gabatar da hujjojin da za su hana Maryam Sherif rike yaranta ba

Wata babbar kotu da ke Kubwa a Abuja, ta umarci Alhaji Atiku Abubakar da ya mayar wa Maryam Sherif, tsohuwar matarsa yaransu 3 da ke hannunsa take-yanke.

A shekarar da ta gabata ne Maryam ta maka Abubakar kotu, inda take bukatar ya bata yaransu maza 3 da yake rike dasu.

Abubakar da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Alkalin kotun, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai bayar da wata hajja a musulunce da za ta hana uwar amsar yaranta ba. Amma zai iya daukaka kara cikin kwanaki 30.

A kotun, Maryam da lauyanta, Nasir Sa'idu sun halarci zaman, yayin da Abubakar da lauyansa , Abdullahi Hassan kuwa basu je ba.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Abinda Buratai ya sanar da kwamandojinsa a taronsu na ranar Litinin

Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3
Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)

A wani labari na daban, Masarautar Karaye da ke jihar Kano ta sanar da satan matar sarkin kauyen Tsara da ke karamar hukumar Rogo, Aishatu Aliyu da wasu 'yan bindiga suka yi.

Kamar yadda sarkin Rogo (Wamban Karaye), Muhammadu Mahraz, ya kai wa Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II, rahoto, wasu 'yan bindiga sun shiga gidan sarkin kauyen Tsara, Aliyu Muhammad, da misalin karfe 1 na daren Juma'a, inda suka tafi da matarsa.

Kakakin masarautar, Haruna Gunduwawa, ya sanar da PREMIUM TIMES cewa ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka yi ta harbin iska kafin su dauki matar a gaban sarkin kauyen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel