Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar

Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar

- Gumurzu ya hargitse tsakanin masu kwasar kayan tallafi da jami'an tsaro a jihar Lokoja ranar Lahadi

- Bayan jami'an tsaron sun kama su dumu-dumu da kayan abincin tallafin COVID-19 da taki suna shirin gudu

- Tashin hankalin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 4, sannan fiye da mutane 30 sunji munanan raunuka

Babban birnin jihar Kogi, Lokoja ya koma kamar filin daga a ranar Lahadi da daddare, bayan bata-garin da suka je sato kayan tallafin COVID-19 sun gamu da jami'an tsaro masu kulawa da kayan ADP da ma'adanar kamfanoni masu zaman kansu.

Jami'an tsaron sun gamu da bata-garin da suka kwaso taki da shinkafa. Sakamakon gumurzun, mutane 4 ne suka rasa rayukansu, sai mutane 30 har da wani dan jarida da suka ji munanan raunuka.

Shigen lamarin da ya faru a Kogi, ya maimaita kansa a Calabar da Cross River, inda fiye da mutane 10 suka rasa rayukansu, ciki har da wata mata mai juna biyu, inda aka yi ta tafka gumurzu tsakanin bata-gari da jami'an tsaro tun ranar Asabar har Lahadi da daddare.

KU KARANTA: Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)

Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar
Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku dauka mataki a kan masu sata, kada ku saurara musu - Buratai ga Kwamandojinsa

Bayan mutane 10 da suka rasa rayukansu a Calabar, jami'an tsaro sun samu nasarar damkar bata-gari a kalla 80.

Sannan mata 2 sun rasa rayukansu sakamakon damben debo kayan tallafin COVID-19 a wata ma'adanar gwamnati da ke layin sakateriya a wuraren Gwagwalada da ke Abuja.

Sun kwashi kayan abincin ma'adanar Bola Rotimi da sauran manyan 'yan kasuwa da ke jihar Kogi, inda suka kwashi shinkafa.

Wasu daga cikin 'yan ta'addan sun balle ATM din wani banki da ke kusa da layin makabarta, wanda ke kallo wani wurin cin abinci.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel