Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso

Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso

- Wasu matasa sun kawo cikas a wurin raba kayan tallafin jihar Ogun

- Sun tayar da hankulan al'umma kafin su yi awon gaba da kayan

- Tashin hankalin yasa masu rabawar suka tsere suka bar su suna satar

Ana tsaka da raba kayan tallafi a ranar Litinin wasu bata-gari suka dakatar da lamarin, daganan suka kwashe kayan tas sukayi awon gaba dasu, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana labaran jihohin da suka yi ta satar kayan tallafi, sai gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba kayan abincin kananan hukumomin da aka ajiye kayan tallafinsu a Ijebu, wadanda suka hada da karamar hukumar Ode, Sagamu da Ifo.

Masu rabawar da suka taru a Ijebu, sun fara raba kayan abincin kenan sai ga bata-garin, wadanda suka kwashe kayan tallafin suka kara gaba.

Wadanda al'amarin ya faru a gaban idonsu sun ce masu rabon da jami'an sun rasa yadda za su yi da su.

Makamancin haka ya faru a Sagamu, Inda aka ajiye kayan abincin a sansanin masu bautar kasa.

Bidiyon yayi ta yawo a yanar gizo, wanda yake nuna masu satar suna kai kayan abincin wani gini wanda ake zargin wurin bauta ne.

Wani shugaban matasan Sagamu, Kayode Segun Okeowo, ya sanar da manema labarai cewa babu wata sata da aka yi a Sagamu.

Ya ce tabbas matasa sun so kwasar kayan daga ma'ajiyar gwamnati, amma gwamnati tasa tsauraran matakai don gudun karya doka.

Daga baya gwamnati tayi alkawarin raba kayan tallafin nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA: Abinda yasa karnuka basu yagalgala naman wadanda suka yashe gidana ba - Sanata

Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suna buga wawaso
Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suna buga wawaso. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kwara a ranar Litinin ta tabbatar da kamen mutum 144 da ke da alaka da satar kayan gwamnati da na jama'a a Ilorin da ke jihar Kwara.

Bata-gari da suka boye karkashin inuwar masu zanga-zangar EndSARS a Ilorin a ranar sun dinga satar kayayyakin shaguna da na ma'aikatu.

Sun dinga cin zarafin masu ababen hawa da kuma mazauna birnin. A yayin zantawa da manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kayode Edbetokun, ya ce sun yi kamen ne bayan kokarin jami'an tsaro na hadin guiwa a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: